Ya kamata Gwamnatin Taraba ta sa baki a kan matsafan Zing

A ’yan kwanakin nan kuma har zuwa wannan lokaci Jihar Taraba ta shiga cikin labaran kasa, a zamanin da wani rikici mai kama da na addini yake ruruwa, tun bayan mutuwar Maimartaba Sarkin Zing (Kpanti Zing) Alhaji Abbas Ibrahim Sambo, a cikin turmutsitsin jifar Jamrah a ranar Babbar Sallah, wato 24 ga watan Satumbar da […]

Ya kamata Gwamnatin Taraba ta sa baki a kan matsafan Zing
Ya kamata Gwamnatin Taraba ta sa baki a kan matsafan Zing

A ’yan kwanakin nan kuma har zuwa wannan lokaci Jihar Taraba ta shiga cikin labaran kasa, a zamanin da wani rikici mai kama da na addini yake ruruwa, tun bayan mutuwar Maimartaba Sarkin Zing (Kpanti Zing) Alhaji Abbas Ibrahim Sambo, a cikin turmutsitsin jifar Jamrah a ranar Babbar Sallah, wato 24 ga watan Satumbar da ya gabata, turmutsitsin da ya zuwa yanzu ake kyautata zaton mahajjat sama da 2,000, suka mutu, inda mahajjatan kasar nan 222, suke cikin wannan jimla, baya ga daruruwan da suka jikkata wasu kuma daruruwan suka bace. Shi dai Kpanti Zing, shi ne Amirul Hajj na Mahajjatn Jihara Taraba, ya kuma mutu tare da wasu matansa biyu da sauran iyalansa biyar.

Tun bayan rasuwarsa ne ana cikin tsakiyar zaman makoki wasu gungun masu addinin dodanni su sama da 200, daga sassa daban-daban na Masarautar ta Zing (an ce ma har da rakiyar na wasu sassan jihar), suka kutsa kai cikin fadar ta Kpanti Zing, inda suka yi nasarar tarwatsa masu zaman makoki da ma sauran iyalan Sarkin na Zing da ke cikin fadar, da sunan su na boren lallai sai a dole a wannan karon an nazairin su a zaman sabon Sarkin na Zing. Har ya zuwa wannan lokaci da aka samu sama da wata guda da mutuwar Sarkin na Zing, rahotanni sun tabbatar da cewa masu bautar dodannin suna cikin fadar Sarkin na Zing, sun yi zaman dirshan, suna ta kara kawo bazarana ga al`ummar garin da kewaye da harkokinsu na yau da kullum, ba tare da samun wata kyakykyawar tsawatarwa ba ta daukar kwararan matakan tsaro da nufin kawo karshen mamayar, balle a za a nada sabon Sarki, ballantana kuma harkokin yau da kullum su samu dawowa kamar yadda suke a da a garin na Zing da kewayensa.
Da yadda rahotanni suke fitowa daga Zing, ka iya cewa ba wanda zai ce ma ga lokacin da za a kawo karshen wannan mamaya ta masu dodanni. Hakan kuma bai rasa nasaba daga irin yadda ake ganin Mahukuntar Jihar Taraba su na yi wa batun biris da nuna halin ko in kula, al`amarin da ya ke kara karfafa zargin mutanen garin na Zing da ma na jihar da na kasa baki daya, cewa, Mahukuntan Jihar Taraba da ma na karamar Hukumar Zing suna da hannu a cikin abubuwan da masu bautar dodannin suke yi a fadar ta Zing. Alal misali, tun bayan mamaye fadar ba wani kwakkwaran mataki na yin jan ido da gwamnan jihar, Mista Darius Ishaku ya nuna wajen ganin an kawo karshen dambarwar, balle kuma a ce an kamo bakin zaren kan yadda za a samu nada wani sabon Sarkin na Zing daga gidajen Sarauta biyu, wato gidan Sarautar Sambo, inda wannan Sarkin da ya mutu ya fito da gidan Komborankom, gidajen Sarautar da Dokar nada da tube Sarkin na Zing, ta tanadi daga wadannan gidaje biyu, za a rinka zaben sabon Sarkin, idan har bukatar hakan ta taso.
Da tanade-tanaden wancan doka da kuma ikon da Mahukuntan Taraba suke da shi, me ya kawo a ce har mahukuntan sun yi sakaci, wajen kasa kawo karshen mamayar da masu bautar dodannin suka yi wa fadar ta Zing? Me kuma ya kawo maimakon Gwamna Ishaku na Taraba ya tabbatar da daukar dukkan irin matakan da suka kamata ko da kuwa ta yin amfani da karfi ne tun farkon mamayar, wajen fatattakar matsafan duk da irin dimbin ikon da ya ke da shi na tabbatar da tsaron doka da oda a jiharsa? Maimakon daukar matakan da suka dace, sai kawai gwamnan ta hannun Babban Sakataren Ma`aikatar kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Bello Yero, ya ba da shelar nada Wazirin Zin Mista Linus Ibrahim a matsayin Wakilin gari. Sanarwar tasa ta kara da cewa gwamnan jihar ya yi wa jami`an tsaro cikakken bayani a kan yadda za su tafiyar da zaman lafiya da bin doka da oda a garin na Zing. Abin tambaya a nan shi ne ko haka dokar nadawa da tube Sarkin na Zing ta tanada, wato a nada Wakilin Sarki, kuma a ba jami`an tsaro umurnin yadda za su gudanar da ayyukansu?
Tabbas, daga yadda al`amurra ta fannin tsaro suke gudana a garin na Zing, jami`an tsaron sun dauki umurnin gwamnatin jihar, don kuwa an ruwaito Kakakin Rundunar `yan sandan jihar, DSP Joseph Kwaji yana fada wa manema labarai a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, cewa, bayan tura karin `yan sandan kwantar da tarzoma da aka yi a garin na Zing da suke sintiri ba dare ba rana, gwamnan jihar kuma ya kafa dokar hana zirga-ziga a garin. DSP Kwaji, wanda tun farko ya ki ya amince da cewa akwai ma wasu masu bautar dodanni da suka mamaye fadar ta Sarkin na Zing, bare ma ya amsa tambayar lokacin da ya ke jin za a fitar da su daga fadar da ma garin baki daya.
Zuwa yanzu Gwamnatin Jihar Taraba ta yi gum da bakinta akan wannan dambarwa ta Zing, yayin da shi kansa Shugaban karamar Zing, Malam Konko, ya bayyana wa Wakilin wannan jarida na Jihar Taraba, ta waya cewa shi ba zai yi magana ba a kan abubuwan da suke wakana a Zing, domin gwamnatin jihar ta hana shi cewa uffan. Duk da Mahukuntan, sun hada baki da jami`an tsaro sun ki daukar matakan da suka kamata wajen kawo karshen wannan fitina da a kullum take kara ruruwa, amma dai mutanen masarautar ta Zing (wadanda tuni wasu musulmansu suka kaurace wa garin na Zing) da na jihar ta Taraba da ma wasu na cikin kasa, suka magantu cikin zargin mahukuntan jihar suna da hannu da matukar sha`awa a kan wannan dambarwa ta kutsa kai da yin zaman dirshan din matsafan a cikin fadar Sarkin na Zing, al`amarin da ya zuwa yanzu batun zaben sabon Sarkin ya gagara.
Wannan goyon bayan mahukunta, ya kara jefa dukkan Sarakunan Musulunci na jihar da sauran al`ummar Musulmi, musamman na jihar, cewa daga yanzu duk inda sarautar wani sarkin Musulunci ta samu a Jihar Taraba, to, kuwa Kirista za a nada, musamman a tsarin zamantakewar da ake ciki a jihar ta Taraba ta kashi 40 na al`ummar jihar musulmi ne, wani kashi 40, kuma Kiristoci ne, yayin da sauran 20, na masu bautar dodanni ne, wadanda sun fi alaka ta kut-da-kut da Kiristoci, don haka Musulmi suke marasa rinjaye, shi ya sanya ma `yan takarar neman mukamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar APC, Sanata Jimmai Alhassan ba ta kai labari ba, duk da zagaye na biyu da aka yi ita ta ba gwamna mai ci yanzu na PDP.
Kodayake Jihar Taraba ba ta da tarihin rincabewar fadace-fadace irin na addini kamar yadda ake fama da su a jihohi irin su Filato da Kaduna, wannan kuma bai rasa nasaba da irin tsarin zamantakewar al`ummar jihar suke ciki, wadda da wuya a iyali ka tarar zaman zalla Musulmi ko zalla Kiristoci suke. Ko kusa ba fata nike wa Jihar Taraba da mutanenta ba, amma akwai fargabar cewa muddin mahukuntan jihar ba su jajirce ba a wannan karon wajen kawo karshen wannan mamaya ta masu bautar dodannin fadar Sarkin na Zing ba, to kuwa za ta iya zama wata kafa da wasu za su sake yin haka a duk lokacin da dama irin wannan ta samu. Allah Ya kiyaye.