‘Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta tausaya wa wadanda ’yan Boko Haram ke halakawa’
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Mustapha, ya ce kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta nuna tausayi da damuwa game da rayukan mutane da suke salwanta a dalilin barnar da ’yan Boko Haram ke yi a jihohin Borno da Yobe tare da nemo hanyar magance matsalar da ta haifar da kauracewar dubban mutane daga garuruwansu […]
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Mustapha, ya ce kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta nuna tausayi da damuwa game da rayukan mutane da suke salwanta a dalilin barnar da ’yan Boko Haram ke yi a jihohin Borno da Yobe tare da nemo hanyar magance matsalar da ta haifar da kauracewar dubban mutane daga garuruwansu baya ga asarar dimbin rayuka da asarar dukiya mai yawa.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala taron gwamnonin APC a Ibadan a ranar Litinin, Mataimakin Gwamnan ya ce,”Maganar sauke Gwamna daga kujera domin nada kantoman soja a jihar da wasu kafofin labarai suka yayata cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi zancen banza ne, domin babu dimokuradiyya ke nan. Harkokin tsaro a halin da ake ciki suna hannun sojoji ne, saboda haka idan har da gaske ake yi to, sai a wadata sojojin da makaman da za su iya fuskantar wadannan mutane domin an san su kuma an san maboyarsu, mene ne dalilin da zai sa a kyale su suna ta kashe mutane da kwace abinci da dukiyoyi suna barinsu cikin halin tagayyara ba tare da an yi maganinsu ba?”
Ya kara da cewa: “Mu da muke zaune a cikin wannan jiha mu ne muka san irin mutanen da suke kai-kawo a kowane sako, kuma tunda harkokin tsaro ya fice daga hannunmu a dalilin dokar ta-baci, mun yi iyakar abin da ya kamata mu yi ta fannin bada cikakken bayani dangane da wadannan mutane da maboyarsu, amma idan ka kawo mutumin da bai san komai ba, ai babu abin da zai iya yi sai ma ya kara lalata abubuwa.”
Alhaji Zanna Musatapha ya ce, “Wallahi muna cikin wani irin hali da ba ya da kyau ko kadan a Jihar Borno, ba mu taba ganin irin wannan ba a rayuwarmu, an kashe mutane a garuruwa daban-daban an kona musu gidaje an kwace abincinsu, sai dai mun ci gba da rokon Allah Ya yi mana magani.”
Mataimakin Gwamnan ya ce, ba rashin aiki ne ya jefa ’yan Boko Haram cikin wannan al’amari ba. “Maganar Boko Haram, rashin hankali ne na wasu yara da suka dauki wata mummunar akida da ba mu san kanta ba, suke kashe mutane ba gaira ba dalili. Akwai irinsu da aka kama da suka tabbatar da cewa, tuni suka bar aikin Allah yanzu aiki suke yi na son zuciya,” inji shi.