Ya kamata gwamnoni su rika tausaya wa jama’a – Maikwai

Shugaban kungiyar Dattawan Bauchi ta Kudu, Alhaji Garba Maikwai ya bukaci gwamnonin kasar nan su tallafa wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen tausaya wa talakawa musamman biyan hakkokin ma’aikata da ’yan fansho. Alhaji Garba Maikwai ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Bauchi, inda ya ce a yayin da Shugaban kasa […]

Ya kamata gwamnoni su rika tausaya wa jama’a – Maikwai

Shugaban kungiyar Dattawan Bauchi ta Kudu, Alhaji Garba Maikwai ya bukaci gwamnonin kasar nan su tallafa wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen tausaya wa talakawa musamman biyan hakkokin ma’aikata da ’yan fansho.

Alhaji Garba Maikwai ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Bauchi, inda ya ce a yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokarin warware matsalolin da suka dabaibaiye kasar nan, gwamnonin suna da gudunmawar da za su bayar wajen saukaka wahalhalun da jama’a suke sha.

Ya kawo misali da kudin Kulob din Paris da Shugaba Buhari ya biya jihohi domin su biya fansho da garatuti a wani bangare na sassauta matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan, inda ya ce, “Ya kamata gwamnonin jihohi su fahimci cewa wadannan kudade an yi alkawari da su ne kan za su biya fansho da garatutin da tsofaffin ma’aikata suke bin jihohin shekara da shekaru. Don haka su yi kokari su biya wadannan hakkoki domin sassauta matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar nan. Mun yarda cewa hakkokin jihohin ne, to amma su ma gwamnonin su tuna tsofaffin ma’aikata hakkokinsu suke nema a biya su.” 

Alhaji Garba Maikwai ya ce, duk Gwamnan da ya gaza biyan ma’aikata ko fansho da garatuti yana jawo wa Gwamnatin Tarayya da Shugaba Buhari ke jagoranta da gwamnatocin jihohi na Jam’iyyar APC bakin jini ne. Kuma idan jama’a suka tashi kuka da jam’iyyar da jami’anta za su yi wanda kuma zai shafi su gwamnonin da ita kanta jam’iyyar a zabe mai zuwa.