Ya kamata ku san Tinubu ciki da waje
Ana ganin Tinubu ya yi tasiri wajen hada kan bangarorin APC domin kai Buhari ga nasara a karon farko a 2015.
Bola Tinubu, wanda a siyasa ake wa lakabi da “Uban gidan siyasa” ya yi suna wajen kwarewa da kafuwa da kuma kwazonsa, sannan bai taba boye burinsa na zama shugaban Najeriya ba.
A watan Janairu lokacin da ya bayyana shirinsa na ganin jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben 2023, Tinubu ya ce zai cika wani buri na “rayuwa”.
- Tinubu ya gana da Gwamnonin Arewa kan batun daukar Mataimaki
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana
- An ga dan Saurauniyar Ingila yana tallan mujalla a kan titi
A yanzu dai Bola Tinubu mai shekara 70 na shirin a nuna kwanjinsa bayan ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani, ya zama dan takarar shugaban kasa a APC a zaben 2023.
Zai fafata da dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar a zaben da zai gudana a watan Fabrairu, 2023.
Gogaggen dan siyasa
Tinubu, wanda kuma ake yawan kira da ‘Jagaban’ — wanan wata saraunta daga Jihar Neja — ya kwashe shekaru yana fadada alakarsa, daga Jihar Legas zuwa fadin Najeriya baki daya.
Ana ganinsa a matsayin jajirtacce, mai fikira da tasiri gami da gwanancewa wajen dabarun siyasa.
Yana daga cikin ’yan siyasar da suka kafa jam’iyyar AD tare da daukar nauyinta; Daga baya ta koma ACN sannan daga bisani ta hade da wasu bangarori aka samar da jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Ana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan bangarorin APC domin ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe a karon farko a 2015.
Nasarar Buhari a 2015 ne ya ya kawo karshen shekara 16 na mulkin Jam’iyyar PDP, tun 1999 da Najeriya ta dawo Jamhuriya ta Hudu.
Zai fafata da Atiku
Zaben tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wanda ya dade yana neman shugabancin Najeriya, a matsayin dan takarar PDP na shugaban kasa a zaben 2023 ke da wuya, Tinubu ya yi gaggawar bayyana kansa a matsayin wanda zai kai iya karawa da shi.
“Ina fatan fafatawa da shi a matsayin wanda ya cancanta a zabe mai zuwa,” in ji shi.
Dan gwagwarmaya
Tinubu wanda Musulmi ne kuma haifaffen yankin Yarabawa a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, ya yi karatu a kasar Amurka, inda ya samu horo a matsayin akanta.
Ya kuma yi aiki da wasu kamfanoni na Amurka, ciki har da ma’ajin kudi a kamfanin mai na ExxonMobil.
Ya kasance dan gwagwarmayar siyasa kafin daga bisani ya zama Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Jihar Legas, sannan daga baya ya zama Gwamnan Jihar Legas na tsawon shekara takwas, daga shekarar 1999 zuwa 2007.
A lokacin da yake gwagwarmaya, tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya yi kaura tare da wasu masu fafutikar neman komawa mulkin dimokuradiyya a 1999.
Tasirin Tinubu
Ana ganin Tinubu ya yi tasiri matuka wajen cin zaben Buhari, nasarar farko da ’yan adawa suka samu a kan gwamnati mai mulki a Najeriya.
Haka kuma ana ganin sake zaben Buharin da aka yi a babban zaben 2019 a matsayin wani bangare na tasirin siyasar Tinubu.
A matsayinsa na Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, ana ganin tasirin Tinubu a kusan duk shawarar da jam’iyyar take dauka, haka kuma, samun goyon bayansa na da matukar muhimmanci ga cim ma burin kowane dan takara.
Rike madafun iko
Game da ke rike da madafun iko, Tinubu ya yi wa kujerarsa ta Gwamnan jihar Legas kyakkyawan riko tun daga 1999 har zuwa 2007.
Bugu da kari, yana da yana da hannu sosai wajen zabar wadanda za su gaje shi tun bayan da ya bar mulki.
A lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas, dangantakarsa ta yi tsami da Gwamnatin Tarayya, a lokacin Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.
Sai dai kuma, Tinubun yana yawan yin zaman doya da manja tsakaninsa da mataimakinsa.
A karshen wa’adinsa biyu a Legas, Tinubu ya zabi daya daga cikin na hannun damarsa, Babatunde Fashola, domin ya karbi ragamar mulki.
Karfin Tinubu a Kasar Yarabawa
Tasirin Tinubu a yankin Kudu maso Yamma, mai magana da harshen Yarbanci, abu ne da wadansu masu son zama ’yan takara da suka rasa manyan mukamai suke adawa da shi.
Suna kuma zargin sa da cewa mutum ne mai mulkin kama-karya da rashin bin tsarin dimokuradiyya.
“Tinubu yana da na’ura tafiyar siyasa mai karfi da kuma tsauri sosai,” in ji Dapo Thomas, malamin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Legas.
Zargin rashawa
Kamar yadda siyasar Tinubu ke yawan kawo cece-kuce, haka ma harkokinsa na kudi.
Ana kyautata zaton yana daya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya.
Bayan ya bar mulki a matsayin Gwamnan Jihar Legas, an tuhume shi da almunda, amma daga baya kotu ta wanke shi daga duka zargin da ake mishi na almundahana da karkatar da kudade da kuma gudanar da asusun ajiyar bankunan kasashen waje sama da goma.
Ko da yake ba a san ainihin tushen arzikinsa ba, amma yana da hannun jari a harkokin kasuwanci da dama, kamar kamfanonin watsa labarai da harkar sufurin jiragen sama, otal-otal da gidaje da kuma tuntubar haraji.
Wani mai adawa da shi ya bayyana shi a matsayin ‘dan siyasa mai hadama’ wanda ya rike makogwaron manyan hanyoyin samun kudaden shiga a Legas.
Sai dai Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, wanda shi ne tsohon Shugaban Ma’aikatan Tinubu, ya dage cewa tsohon uban gidan nasa yana daya daga cikin ’yan siyasa masu kaifin basira.
“Babu wani dan siyasa a Najeriya a yau da ke da irin karfin yin aikinsa, hakurinsa da hangen nesa da jajircewarsa da kishinsa na sadaukar da kai,” inji shi.
Lafiyar Tinubu
An yi ta cece-ku-ce game da lafiyar Tinubu a shekarar 2014 bayan bullar hotonsa ya jeme, a lokacin da ya dawo daga wata tafiya kasar waje da ba a fayyace ba; Amma Jam’iyyar APC ta musanta cewa ba shi da lafiya.
A shekarar 2021 da ta gabata, ya shafe watanni da dama a birnin Landan na kasar Birtaniya yana jinya, wanda ofishinsa ya ce an yi mishi tiyata ne a gwiwa.
Sai dai kuma wani alamar tasirinsa, shi ne yada tawagar shugabannin siyasa Najeriya ke ta zaryar zuwa su ziyarce shi a can, ciki har da shi kansa Buhari.