Ya kamata kungiyoyin tsofaffin dalibai su dunkule wuri daya – Shugaban Serbicecom
An yi kira ga kungiyoyin tsofaffin daliban makarantu da ke Jihar Kano su hade su zama tsintsiya madaurinki daya ta hanyar kafa babbar kungiya don magance matsalolin da makarantunsu suke fuskanta. Shugaban Hukumar Tabbatar da Ingancin Ayyuka ta Jihar Kano (Serbicom) Alhaji Abdullahi Musa ne ya yi wannan kira a lokacin da yake ganawa da […]
An yi kira ga kungiyoyin tsofaffin daliban makarantu da ke Jihar Kano su hade su zama tsintsiya madaurinki daya ta hanyar kafa babbar kungiya don magance matsalolin da makarantunsu suke fuskanta.
Shugaban Hukumar Tabbatar da Ingancin Ayyuka ta Jihar Kano (Serbicom) Alhaji Abdullahi Musa ne ya yi wannan kira a lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyoyin tsofaffin dalibai da ke jihar da sauran masu ruwa-da- tsaki a harkar ilimi.
Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa ta hanyar wannan hadin kai ne kungiyoyin tsofaffin daliba irin su KASSOSA suka samu kaiwa inda suke a yanzu, “Tsofaffin daliban makarantun kimiyya da ke jihar nan da ake kira da KASSOSA abin misali ne domin lokacin da suka hade kansu a karkashin inuwa daya sun samu damar taimaka wa makarantunsu a kungiyance fiye da lokutan baya da suke gudanar da ayyukansu a matsayin daidaikun kungiyoyi. Shi ya sa sauran makarantun da ke jihar muke so su yi koyi su samar da babbar kungiya yadda za su rika magana da murya daya hakan zai ba su damar cimma burinsu na kula da makarantun da suka fito,” inji shi.
Shugaban ya ce kasancewar hukumarsu tana da ruwa-da-tsaki a kowane bangare na tafiyar da rayuwar dan Adam ya sa suka damu da halin da ilimi ke ciki a jihar tare da kokarin lalubo hanyoyin da za a mgance matsalolin da suka shafi cinkoso a aji da rashin kwararrun malamai da rashin kayan koyo da koyarwa. “Hakan ya sa muka hada kai da Hukumar DFID don ganin an fuskanci harkar ilimi ta yadda za a kawo gyare-gyare a makarantun da ke jihar,” inji shi.
Ya ce yanzu harkar kungiyoyin tsofaffin dalibai ta wuce batun zumunci a tsakanin dalibai, inda ya ce “Abin da yake gaban kungiyoyin tsofaffin dalibai ya wuce batun zumunci a tsakaninsu da taimakon junansu, ya kamata su san cewa suna da rawar takawa a wajen ci gaban ilimi. Akwai bukatar su duba makarantunsu, don ganin halin da suke ciki da lalubo hanyoyin da za su tallafa wa makarantun ta hanyar samar da kayan aiki ga malamai da inganta rayuwar daliban makarantun.”
Alhaji Abdullahi ya kuma shawarci kungiyoyin tsofaffin daliban su zama masu jajircewa tare da cire son kai a cikin harkokinsu don ganin an cimma nasarar da aka sanya a gaba.