Ya kamata ma’aikatar ilmi ta ta tallafa wa masu sana’ar dab’i – Ibrahim Ibzar

Alhaji Ibrahim Abdullahi Muhammad Ibzar shi ne Shugaban Kamfanin dab’i  na Ibzar  da ke garin Jos babban birnin jihar Filato.  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana mahimmancin sana’ar dab’i da wallafa ga al’ummar kasar nan. Haka kuma ya bayyana cewa matakin da ma’aikatar ilmi ta tarayya ta dauka na bai wa […]

Ya kamata ma’aikatar ilmi ta ta tallafa wa masu sana’ar dab’i – Ibrahim Ibzar

Alhaji Ibrahim Abdullahi Muhammad Ibzar shi ne Shugaban Kamfanin dab’i  na Ibzar  da ke garin Jos babban birnin jihar Filato.  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana mahimmancin sana’ar dab’i da wallafa ga al’ummar kasar nan. Haka kuma ya bayyana cewa matakin da ma’aikatar ilmi ta tarayya ta dauka na bai wa kananan kamfanonin dab’i da wallafa na kasar nan ayyukan dab’i da wallafa zai bunkasa wannan sana’a  a Najeriya.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Aminiya: Mene ne wannan sana’a ta dab’i da wallafa ta kunsa?

Ibrahim Ibzar: Wannan sana’a tana da  tarihi kuma ta kunshi abubuwa masu tarin yawa. Domin an fara wannan sana’a ce tun a karnoni da dama da suka gabata.

Wannan sana’a wadda take da alaka da  buga takardu, ta  shafi al’umma baki daya ta bangarori da dama. Domin  babu wata ma’aikata ta gwamnati ko ma’aikata  mai zaman kanta, ko makaranta ko wani dan kasuwa  ko wani ma’aikaci ko wani dalibi da ba ta shafa ba.

Kuma yanzu abubuwan da aka fi gudanarwa a wannan sana’a sune buga takardun makarantu, littafai, takadun  aure, takardun suna, takardun bukuwa, takardun  kiwon lafiya,  takardun fastocin ‘yan siyasa,  kalandu,  rahotannin shekara-shekara, takardun jarrabawar makarantu da dai sauransu.

Aminiya: Wanne irin mahimmanci ne wannan sana’a take da shi ga al’ummar kasar nan?

Ibzar: Babu shakka  wannan sana’a tana  da matukar mahimmanci ga al’umma kuma tana ba da gudunmawa wajen samar wa matasa ayyukan yi a kasar nan. Domin a duk inda ka ga  ana gudanar da wannan sana’a za ka ga mutane da yawa,  suna gudanar da ayyuka daban daban na wannan sana’a. Saboda tana da bangarori da dama tun daga bugawa zuwa kammalawa.  Kuma wannan sana’a tana taimakawa wajen bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan.  Tun daga saye takarda da tawada da sauran sinadarai na aiki. Kadan ke nan daga cikin mahimmancin wannan sana’a.

Aminiya: Wanne hali ne wannan sana’a  take ciki a wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari?

Ibzar: A gaskiya wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari ta dauko matakai na tallafawa masu wannan sana’a musamman  kananan kamfanonin dab’i da wallafa  na kasar nan, har da manya. Domin wannan gwamnati ta bangaren ma’aikatar ilmi ta tarayya wadda ministan ilmi Malam Adamu Adamu yake jagoranta,  ya bayar da dama ga dukkan bangarorin ma’aikatar ilmi ta tarayya, wajen ganin sun fadada kwangiloli don shiga da  kananan kamfanonin  dab’i da wallafa ayyukan dab’i da wallafa na bangarorinsu, maimakon  takura abubuwa wajen ba wasu shafaffu da mai da ba su fi kamfanoni 10  ko kasa da haka ba.  

A kalla an bai wa kananan kamfanonin dab’i da wallafa sama da 300 wannan aiki, na buga littafan da ake koyarwa a makarantun firamare da sakandare na kasar nan. Wadannan kamfanoni suna nan suna cigaba da wannan aiki  da aka basu ta hanyar ’yan kwangila. Kafin a ba da wannan umarni akwai mawallafa sama da 600, wadanda  sun rubuta littafai amma ba a buga su ba, domin ba su da hanyar bugawa. Amma yanzu irin wadannan littafai da aka rubuta suna daga cikin irin ayyukan da aka bai wa wadannan kamfanoni su je su buga su kawo, don a raba  a makarantun kasar nan.

Babu shakka wannan mataki da ministan ilmi Malam Adamu Adamu ya dauka tare da hadin kan babban sakataren hukumar ilmin bai-daya [UBEC] Dokta Hameed Bobboyi da sauran ma’aikatansu  ya bude kafa ta tallafa wa irin wadannan kananan kamfanoni, wadanda a da ba a yi da su. Kuma  wannan mataki ya bai wa irin wadannan  kamfanoni dama wajen  farfado da harkokinsu tare da ba su dama wajen samar da karin guraben ayyuka ga al’ummar kasar nan. Yanzu idan ka shiga cikin garuruwan Abuja da Kaduna za ka ga wuraren ayyukan buga littatafai da takardu sun cika ana ta ayyuka, sakamakon wannan mataki da aka dauka. Babu shakka wannan abin koyi ne da ya dace sauran bangarorin gwamnati su dauka a matsayin kalubale.

Don haka muna godiya ga wannan gwamnati, domin ba a taba samun gwamnatin da ta tallafa wa kananan kamfanonin dab’i da wallafa kamar wannan gwamnati ba. Domin a gwamnatocin da suka gabata ba a maganar irin wadannan kamfanoni, sai manya kadai.

Babu ma’aikatar gwamnatin da babu wurin da masu dab’i da wallafa da ba za su yi mata aiki ba.  Yin haka zai dada bunkasa wadannan kananan kamfanoni kuma za a samu ayyukan yi da yawa a wadannan kananan kamfanoni na dab’i da wallafa.

Aminiya: Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga masu wannan sana’a musamman masu kananan kamfanoni irin naku?

Ibzar: Ina kira ga masu wannan sana’a su rike gaskiya da amana kuma su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan wannan sana’a da fadada tunani wajen kirkiro abubuwa masu tasiri da za su amfani kasa baki daya. Akwai tarurrukan da ake shiryawa a Legas a duk shekara don baje kolin sababbin dabarun ayyukan dab’i da wallafa. Yin haka zai taimakawa wajen bunkasa wannan sana’a a matakan jihohi da tarayya da kuma samun gogayya da sauran takwarorin masu wannan sana’a a ko’ina a duniya.