Ya kamata manyan hafsoshin tsaro su yi murabus – Bawa Wase
Wani masanin harkar tsaro Dokta Bawa Abdullahi Wase ya bukaci manyan hafsoshin sojojin kasar nan su yi murabus domin sun zubar da mutuncin kasar nan a idanun duniya.Dokta Bawa Abdullahi Wase ya ce sojojin kasar sun bai wa kasar kunya tare da zubar da mutuncinta, inda suka sanya aikin soja tare da cusa kwamandojin askarawan […]
Wani masanin harkar tsaro Dokta Bawa Abdullahi Wase ya bukaci manyan hafsoshin sojojin kasar nan su yi murabus domin sun zubar da mutuncin kasar nan a idanun duniya.
Dokta Bawa Abdullahi Wase ya ce sojojin kasar sun bai wa kasar kunya tare da zubar da mutuncinta, inda suka sanya aikin soja tare da cusa kwamandojin askarawan kasar cikin harkokin siyasa.
Dokta Wase ya ce idan da shugabannin hukumomin tsaro sojojin kwarai ne tunda aka sanar cewa ba za su iya tabbatar da tsaro ba a lokacin zabe da sun yi murabus. “Idan kuma ba su yi ba, kuma Shugaban kasa da gaske yake zai gudanar da zabe mai inganci da ya sallami shugabannin sojojin daga kan mukamansu. Domin kowanensu ya yi rantsuwa ne cewa zai kare kasar nan ba tare da la’akari da bambancin addini ko yare ko bangaranci ko ba, yanzu abin da kwamandojin suka fada cin amanar kasa ne,” inji shi.
Sai dai ya yi kira ga jam’iyyun adawa da kada su tada hankalin jama’a har ya zamo gwamnati ta samu nasara, ya ce wanda ke kan mulki a yanzu ya gane cewa tabbas idan an yi zabe zai fadi.
Mutane da dama dai na kwatanta matakin da jami’an tsaron suka dauka da juyin mulki, to amma jam’iyyun adawa da masu rajin kare hakkin jama’a sun ce matakin ba zai razana su ba. Sun ce abin da gwamnatin ba ta yi a cikin shekara hudu ba, ta yaya za ta iya yin sa cikin mako shida.