Ya kamata masu mulki su yi koyi da halayen shugabannin da suka gabata – Tsohon Kakakin PDP
Alhaji Bashir Bukar Rimin-Zayam yana daga cikin manyan Jigogin da suka fara afa jam’iyyar PDP, wanda har yanzu yake cikin Jam’iyyar PDP, kuma ya rike Mukamai daban-dabam a cikin jam’iyyar, da suka da Sakataren watsa labaran jam’’iyyar tun daga 1999 zuwa 2007, Ya kuma rike mukamin Kakakin jam’iyyar a Bauchi har zuwa shekarar 2015. A […]

Alhaji Bashir Bukar Rimin-Zayam yana daga cikin manyan Jigogin da suka fara afa jam’iyyar PDP, wanda har yanzu yake cikin Jam’iyyar PDP, kuma ya rike Mukamai daban-dabam a cikin jam’iyyar, da suka da Sakataren watsa labaran jam’’iyyar tun daga 1999 zuwa 2007, Ya kuma rike mukamin Kakakin jam’iyyar a Bauchi har zuwa shekarar 2015. A zantawar da yayi da manema labarai a Bauchi, ya yi bayani game da halin da jam’iyyar PDP ke ciki da kuma dalilan da suka sa ba su barta ba. Ya kuma tabo halin da jam’iyyar APC ke ciki, har ma ya shawarci masu mulki, tare da yin fashin baki kan al’amuran da suka shafi kasar nan.
Aminiya: Tun lokacin da jam’iyyar PDP ta sha kaye a Najeriya mutane ke ganin kamar za ka bar jam’iyyar, sai gashi kana ciki har yau ba abin da ya girgiza ka, ko me ya hanaka barin PDP?
Bashir: Alhamdulillahi, ba wani abu ya hana ni barin jam’iyyar PDP ba sai don mu ne muka kafa ta kuma muka yi ta har muka gina ta ta yi shekaru 16 tana mulki, Allah Ya karba daga hannunta Ya bai wa jam’iyyar APC , to abin da ya hana ni bari, yarda da Ikon Allah, na yarda da Ikon Allah Kwarai da gaske, kuma komi na Allah ne, na kuma yarda da shugabanci, muna kuma biyayya ga shugabanni.
Aminiya: A baya jam’iyyarku ta yi ta fama da rikice-rikice kuma aka yi ta sharia har aka kare.
Bashir: Ai demukaradiyyar ke nan, kowa ya bayyana ra’ayinsa bisa doka, idan kotu ta yi hukunci ko aka kafa gwamnati, sai a dawo kuma a natsu a yafi Juna, asake gina sabuwar tafiyar da za ta kai mu ga nasara, kokarin da muke yi ke nan yanzu.
Aminiya: Yaya za ka bayyana yadda kasar nan take bayan da mulki ya subuce daga hannunku sama da shekaru biyu da suka wuce?
Bashir: Gaskiya abubuwa da yawa sun faru a Najeriya tun da aka fara mulkin nan, kama daga rashin lafiyar shugaban kasa, rikon da mataimakinsa ya yi, wanda ya yi iyakacin kokarinsa, da kuma rikice-rikicen da ita jam’iyya mai mulkin ke fama da su. Maganar da zan yi ta fuskar siyasa ne, bayan an samu mulki da sai a natsu a saurari ’yan takara da masu korafe-korafe da jigogin jam’iyyar da suka ci zabe da wadanda suka fadi, sai a hadu a ga yaya za a gina kasar, a cimma muradun Jam’iyya, a kyauta wa masu zabe. Sai Jarabawa daga Allah Ya zo na tattalin arziki , talauci da yunwa da kuma rikic- rikice tsakanin jigogin jam’iyyar da kuma gwamnoni a jihohinsu, wannan babbar matsala ce da ta kawo tsaiko wajen aiwatar da manufofin gwamnati, Hakika Buhari ya yi kokari, yana da kyakykyawar niyya, amma yanada kura-kurai, haka ma sauran zababbun, kura-kuran ya kamata a gyara, sai a samu karfin da za a kawo cigaban da ya dace.
Aminiya: Wadanne irin rikici ka gani?
Bashir: Ai kowa ya sani, kamar rashin fahimta da ke tsakan in gwamnan Kano Ganduje da tsohon gwamna Sanata Rabi’u Kwankwaso, a Kadunakuma tsakanin Gwamna El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani, haka ma sauran jihohin, yawanci akwai takaddama.
Aminiya: Ta yaya za su gyara ?
Bashir: Sai su yi koyi da irin halayen da shugabanni suka nuna a Jumhuriyya ta farko karkashin Firayim Minista Sa Abubakar Tafawa balewa da shi da Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello, a Jumhuriyya ta biyu kuma akwai shugabanni irinsu Alhaji Shehu Shagari da Dokta Aled Ekweme, su rika jawo jama’a a jikinsu suna saurarensu, su yi kokari wajen ayyukan da za su kawo cigaba, su yaki fatara. Idan suka koyi dabarar mulki irin tasu za a samu nasara.
Aminiya: Idan za ka yi fashin baki kan wadannan ayyuka na cigaba me za ka ce?
Bashir: A gaskiya Buhari yana kokari, misali, mu ’yan Arewa mun samu mukamai da yawa a wannan gwamnatin, wanda mun dade ba mu samu mukamai a tare a waje guda irin haka ba,abin tambaya shi ne,meye wadanda suke rike da madafun iko suka yi ko suka kawo domin ci gaban yankunan su? sai ka tarar babu. Cikinsu duk idan ka cire shugabannin soji, kamar na sojan sama da na kasa, sun yi kokari sun kai rundunonin soji inda babu su a da, da makarantu da asibitoci, yanzu a hukumar Kwastam ko na kamfanin NNPC wane kokari shugabannin wajen suka yi na kai ko da makaranta ce ko wata cibiya a yankunansu domin Jama’a su amfana? sai ka tarar babu. Saboda haka idan har wadanda ke rike da madafun iko za su yi kokari domin su kai abubuwan da za su amfani yankunansu za ka ga Arewa ta ci gaba kuma an samu cigaban kasa ta kowane fanni a lokaci guda.Shi ma
Shugaban kasa akwai bukatar ya kara zage damtse tare da hadin kan ministoci ‘yan arewa da gwamnoninsu, su yi kokari su tabbatar da cewa an samu nasarori kan wadansu daga cikin manyan ayyuka, kamar aikin tonon mai na arewacin kasar nan lallai ne a lokacinsa ya dage ya ga haka ya faru, sai aikin makeken Kamfanin mulmula karafa na Ajakuta da kuma jawo Teku da kuma aikin Samar da wutar lantarki na Mambila da ake yi, wajibi ne suyi duk abin da za su iya domin kammala wadannan ayyuka, yin hakan shi ne zai kawo ci gaban gaske kuma ya sa a yaki talauci, a samar da ayyukan yi . Domin wadannan manyan ayyukan duk a Arewa suke, amma an kasa yinsu , kuma ya kamata a kara himma a farfado da hanyoyin sufurin jiragen kasa domin a samu ci gaba.
Aminiya: Su kuma Gwamnonin wani irin rawa ya kamata su taka?
Bashir: Su rage yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, su zauna a gida su yi wa jama’a aiki, su saurari Jama’arsu, su karbi duk wata suka mai ma’ana da za ta kawo ci gaban yankunansu da kasa baki daya, su tallafa wa duk wasu shirye-shiryen da za su gina jihohinsu. Amma fadace-fadace da kalamun batanci ba nasu ba ne, su hada kan jama’arsu, ciki har da ‘yan adawa, shi ya sa na ce su yi koyi da halayen shugabannin Jamhuriya ta daya da ta biyu. A kowace jiha wadanda suke adawa da juna idan ka bibiya ‘yan’uwa ne, ko wani abu ya hada su a baya , ba za ka ce dangantakarsu kamar ta Zik da su Firayim Minista ba ce, ko ta Awolowo da Shagari ba ce, amma lokacinsu sun martaba juna, sun girmama juna. Ko kwanan nan irin kalaman batanci da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya yi wa Marigayi ’Yar ‘aduwa bai dace ba,ya kamata ya roki gafararsa , don shugaba ne kuma ya rasu, ya kuma yi kokarinsa wajen ci gaban kasar nan, bai kamata bayan rasuwarsa a samu Gwamna mai ci ya rika yi masa kalamun batanci ba, wannan ba daidai ba ne, dole ne El-Rufa’i ya nemi gafarar Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, yakuma nemi gafarar ’yan Najeriya.