Ya kamata matan aure su rage amfani da shafukan sada zumunta – Maryam Umulkhairi
Hajiya Maryam Yahaya Sani ita ce Shugaban Gidauniyar Umulkhairi da ke taimaka wa mata da marayu a Jihar Kaduna. A zantawar da ta yi da Aminiya domin murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, ta koka da yadda mata ke yawan amfani da shafukan sada zumunta. Ko akwai wani tasiri da wannan Rana ta Mata ta […]
Hajiya Maryam Yahaya Sani ita ce Shugaban Gidauniyar Umulkhairi da ke taimaka wa mata da marayu a Jihar Kaduna. A zantawar da ta yi da Aminiya domin murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, ta koka da yadda mata ke yawan amfani da shafukan sada zumunta.
Ko akwai wani tasiri da wannan Rana ta Mata ta Duniya ke da shi ga rayuwar mata?
Wannan rana da aka kebe domin mata na duniya rana ce wadda mu mata muke farin ciki da ita, saboda rana ce da ke ba mu dama mu shirya taro domin tuna wa kanmu abubuwan da suka shafi ci gabanmu da sauransu. Kuma mu duba a ina aka samu koma baya, misali idan aka duba ta wajen ilimin mata an samu ci gaba sosai domin mata sun jajirce wajen harkar koyon ilimi da harkokin sana’ar hannu.
Duk da dai har yanzu ba a kai ga yadda ake son ci gaban ba, domin akwai mata da har yanzu za ka ga ana tauye musu hakkokinsu ta wajen yi musu auren dole, wadansu kuma ana yi musu fyade wanda shi ma matsalace babba ga ’ya mace.
Kuma idan muka duba manyan mata ko matan aure da ke gidajensu musamman idan aka dubi yadda suke tafiyar da rayuwarsu za a ga akwai matsala. Musamman yanzu da aka zo wani lokaci na amfani da Intanet, maimakon mace ta rika koya wa ’ya’yanta karatu idan sun dawo daga makaranta ko rungumarsu ta hanyar nuna musu soyayya sai ka ga ta kwashe lokaci tana duba waya.
Wata sai ta yi awa uku a kan fesbuk ko wassap ko tiwita tana dubawa ba tare da ta kula da ’ya’yanta ba. Wannan abu ne da ke kawo ci baya ga tarbiyyar yara.
Abin da nake nufi a nan shi ne mata su rage amfani da fesbuk da wassap da zai dauki sa’a uku, wanda ba zai kawo ci gaba ga ’ya’yanta ko ita kanta ba.
Amma ta bangaren marayu ko zaurawar da aka bari, shi ma ci gaban kadan ne. Koda irin kungiyoyinmu da muke koya musu sana’o’i, ba mu samun tallafi daga gwamnati wanda za a ce an tallafa mana domin mu samun saukin tallafa musu.
Dama a ce idan mun koya musu sana’o’in za a rika ba su jari, amma sai ka koya wa mutum sana’a amma babu jari ga su da ’ya’ya da yawa marayu. Saboda haka koya wa mata sana’a amma babu jari ba ya da wani tasiri sosai wajen magance matsalolin mata.
A lokacin da ake wannan biki sai ga iyayen ’yan matan Dapchi da aka sace suna cikin bakin ciki. A matsayinki ta uwa ya kike ji?
Gaskiya yadda nake ji shi ne su iyayen wadannan ’yan mata ba su kadai ke kuka ba, har da mu ma a nan mun taya su kuka. Saboda mun san bala’in da ’ya’yansu suka shiga. Babu abin da ya fi wannan tashin hankali a ce an kwashe maka ’ya’ya an tafi da su. Mun taya su kuka kuma Allah Ya dawo musu da ’ya’yansu Allah Ya kiyaye gaba.
Ita kuma gwamnati dole ta kara kaimi wajen magance irin wadannan tsirarun mutane. Domin abin mamaki ne a ce kasa mai yawan mutane sama da miliyan 180 a ce an kasa maganin matsalar.
Don haka ya kamata a hada karfi da karfe wuri guda da jami’an tsaro don kawo karshen matsalar. Ko gidauniyarku ta shirya wani bita domin murnar wannan rana ta mata?
A’a, ba mu shirya wani biki ko bita ba, amma da yake ana gayyatarmu wurare domin murnar wannan rana, mun samu halartar bita da biki da dama. Ka san a duk rana irin ta yau, ana saka kaya mai ruwan goro da fari wato (Pupple and white) idan ka lura ni ma ina sanye da wannan kaya domin murnar zagayowar wannan ranar.
Ko kina da wani jan hankali ga iyaye dangane da kula da tarbiyyar ’ya’yansu?
Jan hakalina gare su shi ne da farko su jajirce wajen koyon ilimi sannan su jajirce wajen tarbiyyantar da ‘’ya’yansu sannan su jajirce wajen ilimin ’ya’yansu. Sannan su yi kokari wajen rage yawan kallace-kallace da kuma yawan amfani da fesbuk da tiwita da wassap domin suna bata musu lokaci sannan suna nesanta ’ya’ya daga iyayensu. Domin wasu lokuta za ka ga yaro na kuka amma ba a kula shi ba.