Ya kamata mu rungumi kishin kasa domin gina kasa
Abu na farko da ya kamata kowane dan kasa ya gane shi ne, kasarka ita ce alkiblar rayuwarka. Abin nufi shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin kasar nan kake. Ya Allah kana cikin kauye ne ko birni, kai dan kasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a karkashin […]
Abu na farko da ya kamata kowane dan kasa ya gane shi ne, kasarka ita ce alkiblar rayuwarka. Abin nufi shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin kasar nan kake. Ya Allah kana cikin kauye ne ko birni, kai dan kasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a karkashin karamar hukuma, a karkashin jiharku; wadanda su kuma suke a cikin Najeriya.
Kasancewar ba ka da wata kasa da ta kai kasarku, lallai ne ka mai da hankali wajen nuna kishinta da kare martabarta, domin kuwa idan ta kasance mai muhibba da martaba, to kai ne ka zama mai martaba da muhibba. Idan kuma ta zama ballagaza, marar kima a idanun duniya, to ka sani kai ma haka kake.
Domin ganin ka zama mutum nagari, mai kima da martaba, sai ka tashi tsaye, ka yi kokari iya yin ka, wajen bunkasa kasarka. Dalili na farko ke nan da ya sanya za ka zama mai kishin kasa. Amma idan zan kara yin wata tambayar kuma, ta yaya za ka zama mai kishin kasa? Ta yaya kishin kasarka zai amfane ka, ya amfani al’ummar kasarka da kuma ita kanta kasar?
Yana daga cikin kishin kasa, ka kasance mai gaskiya da amana a cikin al’amuranka. Idan ka kasance mai fadar gaskiya kuma kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan ka kasance mai rikon amana wajen mu’amalarka da mutane, to kuwa kasarka za ta zama mai gaskiya da amana, abar kauna ga al’ummar duniya. Dalili shi ne, a matsayinka na dan kasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da amana. Idan kai ka zama haka, wancan shi ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; shi ke nan an samu abin da ake so. kasarmu za ta cika da masu gaskiya da amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintatta kuma mai aminci a cikin kawayenta na sassan duniya.
Kishin kasa ne ga dan kasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wanda ba ya aiki ko sana’ar komai. Da zarar dan kasa ya zauna dirshan ba tare da yana wata harka ba, babu wanda zai zame masa aboki sai Shaidan. Wannan zaman banza zai bijiro masa da tunane-tunane marasa kyau, sannan su ingiza shi zuwa aikata munanan ayyuka, wadanda za su kasance halaka a gare shi kuma wadanda za su cutar da sauran al’umma. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi kasarsa, domin kuwa sunanta zai baci ta hanyar munanan ayyukansa.
Don haka, ya dace mutum ya mike tsaye ya sama wa kansa abin yi. Kada mutum ya ce zai zauna sai ya samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Koda ka gama jami’a ne, idan ba ka samu aiki ba, yi kokari ka fara koda aikin karfi ne na kwadago. dan abin da za ka samu, zai iya zama mai albarka kuma ka biya bukatarka da shi. Kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunkuri da ka yi na aikin karfi, Allah na iya hada ka da wata sila, wacce za ka iya samun aikin da ya fi shi.
Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci koda da karamin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya. Sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka rika samu, matukar kana adanawa da kadan-kadan; jarinka yana iya zama mai girma. Idan dai har ka rika gudanar da harkarka cikin gaskiya da tsare hakkin jama’a, kasuwancin naka yana iya zama mai albarka. Domin kuwa, akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da kankanen jari kuma suka bunkasa har suka zama hamshakan ’yan kasuwa.
Ala-ayyi-halin dai, zaman kashe wando, ko zaman jiran mai yawan da ko alamarsa babu, kuma babu tabbas, ba abin dogaro ba ne. Don haka, kishin kasa ne ga mutum ya hana kansa zaman kashe wando, ya cire girman kai daga zuciyarsa, ya yunkura domin neman halal komai kankantarsa.
Kishin kasa ne ga mutum ya kasance mai kaunar jama’a, ba tare da nuna wariyar kabilanci, bangaranci ko addini ba. Kada ka ce za ka yi mu’amala ne kawai da ’yan kabilarka ko ka ce ’yan kabilarka ne kadai mutanen kirki, don haka babu ruwanka da wadansu. Idan ka yi haka, babu shakka ba ka nema wa kasarka alheri ba kuma ba ka zama mai kishinta ba. A lokacin da ka dauki ’yan kabilarka kawai a matsayin mutane, ka banzatar da sauran jama’a, kawai domin su ba naka ba ne, to lallai akwai matsala. Na farko dai, kai kanka za ka gamu da matsala, domin kuwa al’ummar kasarka sun kasance kabilu daban-daban, masu harsuna daban-daban, masu al’adu daban-daban, kuma ya zama wajibi su yi rayuwa tare da wasu kabilun, tunda duk ’yan Najeriya ne. Wata rana, dole ne za ka nemi wata bukata, wacce dan kabilarka ba zai biya maka ita ba. Idan haka ta kasance, to yaya za ka yi, tunda ba ka dauke su a bakin komai ba?
Idan muka duba da idon basira, duk wani addinin da ya amsa sunansa, ba ya son al’umma su nuna kabilanci. Babban burin kowane addinin kwarai shi ne, al’umma su kasance tsintsiya daya, ta yadda za su amfani juna wajen zamantakewa da mu’amala. Hasali ma, Allah (SWT) Ya shaida mana cewa Ya halicci mutane ne zuwa kabilu da jinsuna daban-daban, ba don komai ba sai domin su fahimci junansu. Wannan yana nuna mana cewa, maimakon mu rika nuna kyama da wariya ga kabilun da ba namu ba, kamata ya yi mu fahimci juna, ta yadda za mu amfani juna kuma mu ci gajiyar juna.
Wannan ne ma ya sanya na tuno da wani kalami da wani jigon al’umma, mai kishin kasa da al’ummarsa ya taba furtawa. Ina maganar Gamji dan kwarai ne, wato marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello. Kamar yadda aka ruwaito, an ce marigayi Dokta Nnamdi Azikiwe ne ya taba ce masa su mance da bambance-bambancensu… Shi kuwa Gamji sai ya ce masa ba haka za su yi ba, matukar suna son fahimtar juna.
Kamar yadda aka ruwaito, Sardauna ya ce wa Zik su zo su gane bambance-bambancensu sai su fahimci juna, su yi aiki tare alhali suna masu kiyaye hakkokin juna. Ya ce Zik Ibo ne, shi kuwa Bahaushe. Zik mutumin Kudu ne, shi kuwa dan Arewa. Zik Kirista ne, shi kuwa Musulmi. Ta haka za su hada hannu su yi wa kasa hidima.
Za mu kammala