Ya kamata Musulmi su bubbude makarantun kiwon lafiya da asibitoci – Sheikh Haris Jos
Fitattacen Malamin Addinin Musuluncin nan da ke Jos a Jihar Filato, Sheikh Muhammad Haris Salihu Abubakar Jos, shi ne Daraktan Asibitin Anwar da aka bude kwanakin baya a Jos. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar bude asibitin da muhimmancin bude makarantun kiwon lafiya da asibitoci ga al’ummar Musulmi: Aminiya: […]
Fitattacen Malamin Addinin Musuluncin nan da ke Jos a Jihar Filato, Sheikh Muhammad Haris Salihu Abubakar Jos, shi ne Daraktan Asibitin Anwar da aka bude kwanakin baya a Jos. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar bude asibitin da muhimmancin bude makarantun kiwon lafiya da asibitoci ga al’ummar Musulmi:
Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar gina wannan asibiti?
Sheikh Haris: Abin da ya karfafa mini gwiwar gina asibitin shi ne akwai wani abokina a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna mai suna Malam Muhammad Auwal Bin Usman Saminaka, wanda ya yi kwas a kan harkokin kiwon lafiya. Shi ne ya ba ni shawara kan in bude makarantar horar da kiwon lafiya a nan Jos. Domin irin wannan makaranta za ta taimaka wa al’ummarmu. Don haka, bayan na gina gidana sai na gina masallaci. Daga nan sai na gina wannan makaranta ta horar da harkokin kiwon lafiya. Sai na yi wa wannan aboki nawa magana, cewa ga shi har na gina ajujuwa don bude wannan makaranta. Nan take muka je muka hada hannu da sashin kiwon lafiya na kungiyar malaman makarantun kungiyar Tijjaniyya reshen Jihar Kaduna, wadanda suke da irin wadannan makarantu suka ba mu shawarwari. Muka dauko malamai daga garin Saminaka, saboda akwai reshen makarantar kiwon lafiya ta kungiyar Tijjaniyya a Saminaka. Wato a takaice gina wannan makaranta ta horar da harkokin kiwon lafiya mai suna Anwarul Faidah ne ya karfafa mini gwiwar bude wannan asibiti, wanda muka bude a ranar 1 ga watan Mayun bana.
Aminiya: Kamar yaya matsayin asibitin yake?
Sheikh Haris: Wannan asibiti yana matsayin babban asibiti ne, domin duk abubuwan da ake yi a manyan asibitoci, kan harkokin kiwon lafiya muna yi a asibitin. Domin a dakin tiyatarmu muna da kayayyakin aiki na zamani kuma muna da bangarori guda tara da suka hada da bangaren tiyata da na magani da dakin gwaje-gwaje da bangaren haihuwa da na daukar hoto da sauransu.
Aminiya: Daga lokacin da aka bude asibitin zuwa yanzu yaya ka ga yadda jama’a suka karbe shi?
Sheikh Haris: A gaskiya jama’a suna yaba mana kan yadda muke gudanar da ayyukanmu a cikin rahusa. Domin daga lokacin da muka bude asibitin zuwa yanzu mun yi rajistar marasa lafiya sama da mutum 2000.
Aminiya: Zuwa yanzu wadanne nasarori kake ganin kun cimma?
Sheikh Haris: Mun samu nasara wajen sanya asibitocin da ke wannan gari su rage kudin da suke karba wajen masu jinya, saboda saukin da muke yi wa masu jinya a wannan asibiti.
Aminiya: Mene ne babban burinka kan wannan asibiti?
Sheikh Haris: Babban burina kan wannan asibiti shi ne, in gina mazaunin makarantar kiwon lafiyar. Don haka yanzu na sayi wani fili na kusan Naira miliyan 20 saboda wannan aiki.
Aminiya: A karshe wane sako kake da shi zuwa ga jama’a?
Sheikh Haris: Yanzu bude wannan asibiti kadai da muka yi, kamar yadda na fada tunda farko ya sanya asibitoci sun fara yi wa jama’armu sauki a nan garin Jos. A gaskiya an tafi an bar mutanenmu a wannan bangare na harkokin kiwon lafiya. Don haka ya kamata mutanenmu su tashi su bude irin wadannan asibitoci da makarantun kiwon lafiya, domin taimaka wa al’ummarmu.