Ya kamata Najeriya ta daina biye wa Bankin Duniya da IMF — Jega

’Yan Najeriya sun zargin IMF da tilasta wa Shugaba Tinubu janye tallafin man fetur.

Ya kamata Najeriya ta daina biye wa Bankin Duniya da IMF — Jega

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya gargaɗi Gwamnatin ƙasar da ta kauce wa karɓar shawarwari daga Bankin Duniya da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF.

Farfesa Jega ya ce duk da yake yana da kyau a riƙa hulɗa da waɗannan hukumomin, amma dole ne Gwamnatin Najeriya ta yi taka-tsan-tsan don gudun jefa ƙasar cikin gagarumar matsala.

Tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana haka ne a yayin gabatar da maƙala a wani taron shekara-shekara na manyan darektoci da ke gudana a yanzu haka, yayin da a bana taron ke tattaunawa kan batun samar da ingantacciyar gwamnati domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

Har ila yau, farfesa Jega ya buƙaci samar da sauyi a fannin zaɓen shugabanni, yana mai cewa, babban ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya shi ne cewa, akasarin jagororin ƙasar ba su kintsa karɓar ragamar shugabanci ba.

Jawabin Jega na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan Najeriya ke ci gaba da zargin Bankin Duniya da IMF da hannu wajen jefa ƙasar cikin mawuyacin matsin rayuwa a sanadiyar shawarwarin da suke bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, musamman janye tallafin man fetur da karya darajar takardar kuɗin ƙasar na Naira.

’Yan Najeriya sun zargin IMF da tilasta wa shugaba Tinubu janye tallafin man fetur da kuma karya darajar kuɗin ƙasar.

Aminiya ta ruwaito Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF a makon jiya yana cewa, ba shi da hannu a matakin da Gwamnatin Najeriya ta ɗauka na janye tallafin man fetur a ƙasar.

A yayin zantawa da manema labarai Juma’ar makon jiya a birnin Washington DC na Amurka, Darektan IMF a yankin Afrika, Abebe Selassie ya bayyana matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man a matsayin batu na cikin gida.

“Matakin na cikin gida ne. Ba mu da wani shiri a Najeriya. Rawar da muke takawa ta taƙaita ne kan tattaunawa a kai a kai, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe irinsu Japan ko kuma Birtaniya”, inji Selassie.

Kodayake Selassie ya bayyana cewa, matakin na Gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man na da nasaba da manufofinta na dogon-zango domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

Sai dai IMF ya ce ya lura da irin ƙuncin rayuwar da ’yan Najeriya suka faɗa sakamakon janye tallafin, yana mai shawartar gwamnatin Tinubu da ta samar da hanyoyin rage wa al’umma raɗaɗi.

Shugaba Tinubu dai ya janye tallafin ne jim kaɗan da shan rantsuwar kama aiki a watan Mayun bara.