Ya kamata Najeriya ta fara tsarin mulki na shekara 6, babu tazarce

Ya ce yin hakan zai sa a daina neman tazarce ko ta halin kaka

Ya kamata Najeriya ta fara tsarin mulki na shekara 6, babu tazarce

Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya bayar da shawarar fara amfani da wa’adin shekara shida a kujerar Shugaban Kasa kuma babu neman tazarce.

Hakan, a cewarsa, zai rage neman sake lashe zabe ko ta halin ƙaƙa ga masu rike da kujerar.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa da ya kira a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma bayar da shawarar a rika kammala dukkan shari’un zabe kafin a kai ga rantsar da wanda ya lashe shi.

Ya kuma ce hukuncin Kotun Koli kan nasarar Shugaba Bola Tinubu na makon da ya gabata, ya bar baya da kura matuka.

Atiku dai ya tsaya kai da fata cewa sam Tinubu bai ma cancanci ya tsaya takarar shugaban ba a zaɓen da ya gabata.

Dan takarar ya kuma zargi Kotun Kolin da kuma Hukumar Zabe ta Kasa da goyon bayan rashin gaskiya, damfara da kuma ɗaure wa ƙarya gindi.

A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaben sannan ta yi watsi da ƙarar da Atiku da takwaransa na LP, Peter Obi suka shigar a gabanta suna kalubalantar nasarar.

Atiku dai ya yi wukar kugu da sakamakon binciken da ya ce ya yi a kan takardun karatun Tinubu a Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka, amma kotun ta ce ba ta da hurumin sake karbar sabuwar shaidar da ba a gabatar a kotunan kasa ba.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja