Ya kamata Onnoghen ya nuna babban misali

A ranar Litinin din wannan makon ne Kotun Tabbatar da Da’ar Ma’aikatan Gwamnati (CCT) ta fara sauraron karar da aka kai gabanta ana tuhumar Babban Jojin Najeriya Walter Samuel Onnoghen da laifin kin bayyana dukiyarsa kamar yadda doka ta wajabta wa ma’aikatan gwamnati. Wata kungiya ce a karkashin jagorancin Dennis Akanya, wani tsohon mai taimaka wa […]

Ya kamata Onnoghen ya nuna babban misali

Nkanu Onnoghen

A ranar Litinin din wannan makon ne Kotun Tabbatar da Da’ar Ma’aikatan Gwamnati (CCT) ta fara sauraron karar da aka kai gabanta ana tuhumar Babban Jojin Najeriya Walter Samuel Onnoghen da laifin kin bayyana dukiyarsa kamar yadda doka ta wajabta wa ma’aikatan gwamnati.

Wata kungiya ce a karkashin jagorancin Dennis Akanya, wani tsohon mai taimaka wa Shugaba Buhari ta fuskar watsa labarai kuma dan Jam’iyyar APC a Jihar Enugu ta shigar da karar a kotun tana zargin mai shari’ar da laifin rashin cika ka’idar aiki saboda bai bayyana kadarorinsa ba a lokacin da ya zama Babban Jojin kasar nan.

Shi dai Mai shari’a Onnoghen Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya gabatar wa Majalisar Dattawa da sunansa a matsayin Babban Joji na riko lokacin da yake rike da Shugabancin Kasar nan saboda Shugaba Buhari ya tafi kasar Ingila yana neman magani a shekarar 2016.

A wancan lokaci an yi ta cece-ku-ce kan tabbatar da shi bayan Shugaba Buhari ya samu lafiya ya dawo, domin an yi rade-radin cewa Shugaba Buhari yana so ne ya nada sabon Babban Jojin Najeriya daga cikin lauyoyi, maimakon daga cikin alkalan Kotun Koli da aka saba. Saboda haka sai ’yan yankin Kudu maso Kudu, yankin da Onnoghen ya fito suka tashi tsaye wajen ganin sun tilasta wa Shugaba Buhari ya tabbatar da Onnoghen a kan wannan mukami, domin a ganinsu Shugaba Buhari ba ya son sane  saboda ya fito daga tsirarun kabilun kasar nan.

Onnoghen wanda dan asalin garin Okirika ne da ke Karamar Hukumar Biase ta Jihar Kuros Riba, al’ummar yankin Kudu maso Kudu da sauran mutanen kudancin kasar nan sun yi ta hura wuta lallai sai Buhari ya tabbatar da nadinsa a matsayin Babban Jojin Najeriya tunda shi ne mai mukami mafi girma a Kotun Koli kuma a al’ada wanda ya fi girman mukami a kotun shi ne yake zama Babban Jojin idan an samu gurbi. Sai dai kuma tsarin mulkin kasar nan bai ce dole sai daga cikin alkalan Kotun Kolin za a iya nada Babban Jojin Najeriya  ba, ana iya daukowa daga waje, kamar yadda shugabannin mulkin mallaka suka yi da kuma nada Ayo Irikefe a lokacin mulkin soja wanda aka dauko shi daga jami’a.

Mai shari’a Onnoghen ya gaji Mai shari’a Mahmud Muhammad ne wanda ya yi ritaya a ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamban  shekarar 2016 bayan ya cika shekara 70 a duniya. Domin a ka’ida alkalan manyan kotu suna yin ritaya ne a lokacin da suka kai shekara 70 da haihuwa. Saboda haka shi ma Mai shari’a Onnoghen zai yi ritaya ne a watan Disamban shekarar 2020 lokacin da zai cika shekara 70, wato yana da sauran kusan shekara biyu ke nan.

Wannan ne ya sanya al’ummar Kudu suke ganin Shugaba Buhari ya tsani Onnoghen ne saboda ya fahimci ba zai iya tankwara shi ba shi ya sanya yake neman hanyar da zai kawar da shi kafin a gudanar da zabe.

Saboda Onnoghen ya fito daga yankin Kudu maso Kudu ne ya sanya gwamnonin yankin, in ban da na Jihar Edo wanda dan APC ne, suka umarci Onnoghen da kada ya amsar gayyatar kotun, haka kuwa aka yi, domin Onnoghen bai halarci zaman kotun da aka yi ba a ranar Litinin din da ta gabata.

Haka kuma manya lauyoyi fiye da 150 ne suka ce za su kare Onnoghen a kotun, amma a ranar da aka fara sauraron karar lauyoyi 20 ne suka hallara.

Muhawarar da ake yi a tuhumar Onnoghen a kan hurumin Kotun Da’ar Ma’aikata ne na sauraron karar, inda wadansu ke ganin wai bai kamata a gurfanar da shi a gaban Kotun Da’ar Ma’aikata ba, domin a matsayinsa na Babban Jojin Najeriya wai kamata ya yi a gurfanar da shi a gaban Majalisar Kula da Alkalai ta Kasa (NJC).

A yayin da wadansu kuma ke ganin babu laifi don an gurfanar da shi a Kotun Da’ar Ma’aikata domin shi ma’aikacin gwamnati ne kuma laifin da ake tuhumarsa ba game da wata shari’a ba ce, laifi ne da ya shafi aikin gwamnati.  Yanzu dai an daga sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Janairun nan, wato ranar Talatar makon gobe.

Sai dai kuma wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bukaci Kotun Da’ar Ma’aikatan ta dakatar da sauraron shari’ar tare da umartar Alkalin Kotun Da’ar Ma’aikatan ya gurfana a gabanta a jiya Alhamis domin yin bayani. Abin da yake daure wa mutane kai shi ne wai  idan mutum ya fito daga yankin Kudu shi ke nan ya zama shafaffe da mai ba ya laifi, ya fi karfin doka sai ya yi abin da ya ga dama kuma ya kwana lafiya?

Ana tuhumar Mai shari’a Onnoghen ne da laifin rashin cika ka’idar aikin gwamnati kuma ba cewa aka yi an sauke shi ba, cewa aka yi ya je kotu ya kare kansa, idan ba YA da laifi a wanke shi, to mene ne na tayar da jijiyar wuya game da haka? A matsayinsa na Babban Mai shari’a shi ya fi kamata ya nuna babban misali na mutunta kotu tare da girmama shari’a. Saboda haka ya kamata Mai shari’a Onnoghen ya yi watsi da shawarar da ’yan uwansa na yankin Kudu suke ba shi, ya yi kokari ya halarci zaman kotun a mako mai zuwa domin ya tabbatar wa duniya cewa babu wanda ya fi karfin doka.

Su kuma masu zuga shi kada ya halarci kotun ya kamata su sani fa Mai shari’a Onnoghen ba dansu ba ne kawai Babban Mai shari’a ne na Najeriya kuma mutum na hudu da ke rike da mukami mafi girma a kasar nan.

Mutumin da ya kai karar Onnoghen Kotun Da’ar Ma’aikata dan Jihar Enugu ne, ba dan Arewa ne ba, kuma ya ce sun kwashe shekara guda suna bincike a kan Onnoghen kafin su kai ga daukar matakin maka shi a kotu. Mafita ita ce, a kyale Onnoghen ya je Kotun Da’ar Ma’aikata ya kare kansa. Maganar a tura batun ga Hukumar Kula da Alkalai (NJC) ba ta taso ba, domin Onnoghen a matsayinsa na Babban Mai shari’a shi ne shugaban wannan hukuma domin haka sauran mambobin za su ji kunyarsa a yayin tuhumarsa.