Ya kamata Shekarau ya yi wa Buhari adalci – Ibrahim Fage

An bayyana jawabin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau ya yi a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da cewa abin takaici ne, inda aka shawarce shi ya rika yi wa Buhari adalci. Wani shugaban al’umma Alhaji Ibrahim Abdulkadir Fagge (Mai unguwa) ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa […]

Ya kamata Shekarau ya yi wa Buhari adalci – Ibrahim Fage
Ya kamata Shekarau ya yi wa Buhari adalci – Ibrahim Fage

An bayyana jawabin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau ya yi a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da cewa abin takaici ne, inda aka shawarce shi ya rika yi wa Buhari adalci.
Wani shugaban al’umma Alhaji Ibrahim Abdulkadir Fagge (Mai unguwa) ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Kaduna, inda ya ce Shugaba Buhari ya rungumi mulkin kasar nan a lokacin da babu komai a asusun Gwamnatin Tarayya da na jihohi da kananan hukumomi sai dimbin basusuka.
Ya ce kodayake Malam Shekarau a matsayinsa na dan adawa yana da ’yancin fadin ra’ayinsa, amma idan aka yi la’akari da shekara daya kacal na gwamnatin Buhari babu adalci a yanke kauna ga gwamnati a kokarin da take na tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaro da farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa da ya ruguza kasar nan.
Ya ce shugabannin da PDP ta fitar sun zalunci Najeriya da ’yan Najeriya, saboda ba a taba samun dukiyar man fetur kamar yadda aka samu a shekarun 1999 zuwa 2014 ba, amma abin takaici babu wani ci gaban kasa da ’yan Najeriya suka gani.
Alhaji Fage ya ce Malam Ibrahim Shekarau da ke cewa Shugaba Buhari ya gaza, shi wane ci gaba ya samar wa Jihar kano a shekara takwas da ya yi yana mulkin jihar. “Mu a wajenmu shekara hudu da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yi yana Gwamnan Jihar Kano sun fi shekara takwas da Malam Ibrahim Shekarau ya yi, domin a yau duk wanda ya je Kano birni da kauye ya san cewa ba a kwatanta aikin Kwankwaso da ya mayar da Kano kamar birnin Landan da kuma aikin Shekarau na shekara takwas,” inji shi.