Ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara ministoci?
Ya kamata a canja wasu ne – Muhammadu Auwal Muhammadu Auwal: “A gaskiya in ka yi dubi ta wani bangaren, za ka ga eh, ya kamata ya kara ministoci. A wani bangaren kuma za mu ce wadansu ne yakamata a cikin ministocin a canja su saboda basu bada mahimmanci akan aikinsu. Misali kamar ma’aikatan ayyuka […]
Ya kamata a canja wasu ne – Muhammadu Auwal
Muhammadu Auwal: “A gaskiya in ka yi dubi ta wani bangaren, za ka ga eh, ya kamata ya kara ministoci. A wani bangaren kuma za mu ce wadansu ne yakamata a cikin ministocin a canja su saboda basu bada mahimmanci akan aikinsu. Misali kamar ma’aikatan ayyuka da lantarki da gidaje, ace a hada a waje daya, gaskiya akwai damuwa.Ya kamata kowane ma’aikata yana zaman kansa. Domin yin hakan akwai damuwa da matsololi da cin hanci domin shi wannan ministan, ba zai iya sanin abubuwan da ke faruwa a wasu wuraren ba. Sannan kuma ministocinsa a halin yanzu akwai wadanda har yanzu suna bacci basu ma san meye amfaninsu a wadannan wuraren ba. Ya kamata ya canja su da wasu.”
Ya dace a kara Ministoci – Mubarak Idris Garko
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Mubarak Idris Garko: A ra’ayina game da karin Ministoci, ina goyon bayan yin haka dari bisa dari. Da ma a halin yanzu akwai Ministocin da nauyin da aka dora musu ya yi musu yawa. Alal misali akwai Ministan da ke kula da ayyukan ma’aikatu uku, to ta yaya za a yi irin wannan Minista ya iya gudanar da aikinsa cikin natsuwa da jin dadi? Sannan akwai bangarorin da suke bukatar wakilci amma ba su samu ba, don haka idan aka sake nada wasu sababbin Ministoci akwai yiwuwar irin wannan bangare su samu wakilci a wannan karo, tun da zamani ne na siyasa. Ko ma dai yaya ne samun Ministoci da yawa shi zai samar da ci gaba a kasar mu fiye da yadda ake tafiya a yanzu.
Kada ya kara ministoci – Gyan Pam
Daga Amina Abdullahi, Yola
Gyan Pam: “Ra’ayina shi ne kada ya kara ministoci, amma yana da kyau ya sauke ministocin da ba sa aiki, sannan ya karo wasu wadanda za su maye gurbin wadannan da ya cire. Domin mafi yawancinsu ministocin ana zarginsu da cin hanci da rashawa. Don haka ban goyi bayan ya karo wasu ba sai dai ya rage wasu sannan ya samo wadansu da zasu maye gurbin wadanda zai cire.”
Gaskiya Buhari na bukatar karin ministoci – Tom Garba
Daga Amina Abdullahi, Yola
Tom Garba: “A ra’ayina na dan Najeriya mazaunin Adamawa, yadda na ga yadda shugaba Buhari yake gudanar da aikinsa, gaskiya yana bukatar ma’aikata fiye da wadda yake da su a yanzu. Ma’ana ya kara ministoci. Kin ga yanzu idan aka duba Najeriya, akalla sama da mutum miliyan dari ne. Sannan sai ya rage ministoci. Ni a ra’ayi na kuma a fahimtar kama ludayinsa gaskiya akwai matsala. Matsalar ko ita ce, lokacin da aka kawo ministocinnan aka rage, anzo an soma samun matsala kamar misali, Ministan noma , Audu Ogbe, aka zo aka kara masa wani ma’aikata kuma. Sai a rasa menene makasudin abin da ya kamata ayi. Sannan kuma wadannan ayyukan sun shafe ma’aikatar gudanar da aiki sai a rasa waye ya kamata ya yi wannan aikin idan aikin ya zo. Wadansu ma’aikatar basu da ko ofishi balle teburin da za su zauna su yi aiki a ciki. Hakazalika Ministan yada labarai an zo an hada masa kuma da wadansu a karkashinsa. Sai aga aikin yana ta taruwa. Ni a gani na da bai hada ma’aikata fiye da daya a karkashin ministoci ba, sannan ya sami mutane na gari da za su yi masa aiki.
Akwai bukatar Buhari ya kara Ministoci – Khadija Abdullahi Abubakar
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Khadija Abdullahi Abubakar: Game da tambayar ko Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dace ya kara Ministoci ko a’a? a nawa ra’ayin karin Ministocin ya dace don ko shakka babu zai kawo ci gaba a kasar nan. Dalilin fadin haka kuwa shi ne, duk sassan da ba su samu wakilci a baya ba, yanzu za su samu. Sannan bangarorin da suke korafi a baya na cewa sun tura mota amma ta tafi ta bar su da kura, to akwai yiwuwar a wannan karon za a dama da su. Don haka zai yi kyau Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta karawa da kuma nada sababbin Ministoci don kawo ci gaba a kasar nan da kuma kashe bakin tsanya.
Ban goyi bayan ya kara ba – Ande Emmanuel
Daga Amina Abdullahi, Yola
Ande Emmanuel : “Ba sai an yi karin minista ba. Shugaba Buhari yana son bata rawansa da tsalle ne. Domin shi ya fada mana cewa yana so a takaita kudade don haka ba zai nada ministoci da yawaba. Sai gashi kuma ya dauko ma’aikatu uku ya danka wa Fashola. Tun farko ya ce yana iyakar kokarinsa wajen takaita kashe kudade, me zai sanya shi yanzu ya ce yana son kara ministoci? Wadannan ministocin na yanzu ba wasu ba ne illa ‘yan siyasa masu yi masa kamfe. Idan har shi mutum ne mai magana daya, ya kamata ya tsaya a maganar da ya fada a baya na rashin kara ministoci. Gaskiya karin ministoci a yanzu ba na goyon bayansa, kuma idan har ya kara, kamar ya yi amai ya lashe ne, kuma mutane za su masa kallon dattijo mai magana biyu. A yanzu haka muna fama da yadda za a magance tattalin arziki wadda albashin minista daya ya isa ya ciyar da giwaye goma. Don haka, ban goyi bayan shugaba Buhari ya kara ministoci ba.”