Ya kamata Tinubu ya bayyana kadarorinsa bayan shekara ɗaya a kan mulki — SERAP
Wannan dama ce da Tinubu zai nuna wa ’yan ƙasar yadda yake son ci gaba dimokuraɗiyya da nuna tsantseni.
Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Nijeriya ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da bikin cikarsa shekara guda a kan mulki wajen bayyana kadarorin da ya mallaka.
Cikin wata buɗaɗdiyar wasiƙa da ƙungiyar ta aike wa Tinubu, SERAP ta ce wannan dama ce da shugaban ƙasar zai nuna wa ’yan ƙasar yadda yake son ci gaba dimokuraɗiyya da nuna tsantseni da rashin rufa-rufa a gwamnatinsa.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasar, ya umarci mataimakinsa da ministoci da gwamnonin jihohin ƙasar domin su bayyana nasu kadarorin da suka mallaka.
SERAP ta ce: “Muna so ka wallafa takardun kadarorin da ka mallaka, sannan ka umarci sauran jami’an gwamnati su ma su yi haka, saboda hakan zai ƙarfafa samar da cikakken tsarin gwamnati maras rufa-rufa a duka matakai.”
“Yin abubuwa a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, kamar yadda yake ƙunshe cikin takardun bayyana kadarori, zai inganta tsarin dimokuraɗiyya tare da tsantseni a duka matakan gwamnati,” in ji SERAP.
SERAP ta kuma buƙaci shugaban ƙasar ya gaggauta bijiro da buƙatar yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasar kwaskwarima ta yadda za a saka dokar bayyana kadarorin masu riƙe da muƙamai kafin su hau mulki da kuma idan suna kan mulki da bayan saukarsu.