Ya karya hannun matarsa a kan kunu

Wani magidanci mai suna Muhammed Bello da ke kauyen Sabulari a karamar Hukumar Dutse a Jihar Kaduna ya karya hannun matarsa mai suna Safara Muhammed Bello sakamakon takaddama kan kunu. Majiyar Aminiya ta ce kafin karya wa matarsa hannunta na dama magidancin ya yi wa mata duka kafin ya yi amfani da fartanya wajen karya […]

Ya karya hannun matarsa a kan kunu
Ya karya hannun matarsa a kan kunu

Wani magidanci mai suna Muhammed Bello da ke kauyen Sabulari a karamar Hukumar Dutse a Jihar Kaduna ya karya hannun matarsa mai suna Safara Muhammed Bello sakamakon takaddama kan kunu.

Majiyar Aminiya ta ce kafin karya wa matarsa hannunta na dama magidancin ya yi wa mata duka kafin ya yi amfani da fartanya wajen karya hannunta, sai dai ya ce ya karya hannun nata ne saboda ta kama azzakarinsa tana neman halaka shi saboda ya mare ta sau uku.
’Yan sanda sun gabatar da Muhammed Bello Sabulari a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da matar take amsa tanbayoyin alkali kan zargin kama masa mazakuta ta ce sam ba a yi haka ba, mijin nata yana kokarin kwatar kansa ne daga hannun hukuma ta hanyar yi mata kazafi.
Muhammed Bello ya bukaci kotun ta yi masa afuwa kada ta sake mayar da shi gidan maza, inda ya nemi matar tasa ta yi masa afuwa.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Yahaya Yayari ya ki amincewa da rokonsa inda ya ce laifin da ake zarginsa babban ne a karkashin sashi na 126 na dokokin final Kod, kuma ya saba wa kundin tsarin shari’ar Musulunci da ya ce duk wanda ya karya a karya shi.
Sai ya ce a sake mayar da Muhammed Bello gidan kaso sai ranar Litinin mai zuwa inda za a ci gaba shari’ar don yanke masa hukunci.