Ya kashe abokinsa a kan budurwa
Wani matashi mai suna Guda Amadu ya kashe abokinsa Mustapha Muhammad a kauyen Dau da ke karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano a ranar Litinin da ta gabata ta hanyar yi masa yankan rago. Lamarin ya faru ne misalin karfe 8:00 na dare lokacin da Guda ya iske abokinsa Mustapha yana zance da budurwa da […]
Wani matashi mai suna Guda Amadu ya kashe abokinsa Mustapha Muhammad a kauyen Dau da ke karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano a ranar Litinin da ta gabata ta hanyar yi masa yankan rago.
Lamarin ya faru ne misalin karfe 8:00 na dare lokacin da Guda ya iske abokinsa Mustapha yana zance da budurwa da yake nema mai suna Hadiza, inda ya shiga gaya masa bakaken maganganu a karshe fada ya kaure a tsakaninsu. Majiyarmu da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Bayan sun fara fada ne sai Guda ya zaro wuka ya danne Mustapha ya yanka shi a wuyansa nan take ko shurawa bai yi ba.” kanen mahaifin marigayin Malam dayyabu, ya yi wa Aminiya karin haske da cewa, “Kowa ya san akwai abota a tsakanin matasan biyu, muna gida muna hutawa bayan mun yi buda-baki, sai muka ji labarin cewa Mustapha da abokinsa Guda sun yi rigima a kan budurwa har an yanka shi da wuka. Jin haka ya sa muka garzaya wurin da lamarin ya faru, sai dai ko kafin mu isa ya riga ya cika sakamakon yankan rago da abokinsa ya yi masa.” Kakakin ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin yana hannunsu a sashen kula da manyan laifuffuka. Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.