Ya kashe abokinsa a kan takalmi
Ya amsa cewa ya yi wa abokin nasa haka ne a matsayin ramuwar gayya
Wani matashi mazaunin Unguwar Saunar Nepa da ke Kano ya kashe abokinsa saboda abokin nasa ya sanya takalminsa.
Wanda ake zargin ya shaida wa manema labarai cewa ya aikata laifin ne a wani mataki na ramuwar gayya saboda marigayin mai suna Abubakar Abdulkarim ne ya fara kai masa sara.
- Abin da ya sa sojoji ne ba sa so yaki da ta’addanci ya kare —Sheikh Gumi
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba — Ganduje
- Dalibin aji hudu ya lashe gasar musabakar Al-Kur’ani a Kebbi
- CBN na mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudade – ACF
“Muna zaune bayan mun yi alwala sai ya sanya takalmina, ni kuma sai na nemi ya cire sai ya ki don haka sai na zo na ture shi tare da kwace takalmina.
“Nan da nan sai ya dauko wani karfe ya kawo min suka da shi amma bai same ni ba.
“Ni ma kuma akwai wani karfe a jakata sai na fito da shi na soka masa a gefen cikinsa.
“Ban yi zaton ma ya mutu ba domin a kan idona wani abokinmu ya dauke shi zuwa kemis.
“Sai da dare ne mahaifina yake gaya min cewa ya rasu. Da safe kuma mahaifina ya dauke ni ya damka ni a hannun ’yan sanda.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa bayan da lamarin ya faru an dauki marigayin zuwa Babban Asibitin Muhammad Sanusi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Kiyawa ya kara da cewa kasancewar wanda ake zargin ya amsa laifinsa, abin da ya rage shi ne su gurfanar da shi gaban kotu.