Ya kashe abokinsa da tsitaka
Ana zargin wani matashi mai suna Aminu Umar mai shekaru 19 da kisan abokinsa mai suna Shafi’u Muhammad dan shekaru 18 da haihuwa, inda ya yi amfani da wani abu mai kaifi ya caka masa shi a wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.Rahotanni sun bayyana cewa matasan biyu, wadanda dukkaninsu ’yan asalin karamar Hukumar […]
Ana zargin wani matashi mai suna Aminu Umar mai shekaru 19 da kisan abokinsa mai suna Shafi’u Muhammad dan shekaru 18 da haihuwa, inda ya yi amfani da wani abu mai kaifi ya caka masa shi a wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan biyu, wadanda dukkaninsu ’yan asalin karamar Hukumar garin Isa ne cikin Jihar Sakkwato kuma abokan juna ne da suke zaune a Wapa a karamar Hukumar Fagge, Jihar Kano.
Binciken Aminiya ya gano cewa wata jayyaya ce ta shiga tsakanin abokan biyu, inda a karshe Aminu Umar ya fusata ya dauko wani makami mai kaifi (tsitaka), ya caka wa Shafi’u a makogwaro, lamarin da ya jawo ya fadi yana zubar da jini. Ganin abin da ya faru da Shafiu, sai wanda ake zargin Aminu ya cika wandonsa da iska.
Wani ganau wanda ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da jama’ar suka ga haka sai suka dauke shi zuwa asibiti, inda aka tababtar da rasuwarsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa zuwa yanzu jami’ansu sun cafke sauran abokan zaman mutanen a lokacin da suke kan hanyarsu ta guduwa daga Kano. A yanzu haka dai suna hannunsu, a bangaren binciken manyan laifuka ana bincikensu.