Ya kashe abokinsa kan tukunyar miya

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan Jihar Legas da ke Yaba sun shiga binciken wani matashi dan shekaru 20 mai suna Ngwuta Nweke kan zargin kashe abokinsa da suke zaune tare a daki daya yayin da suke fada a kan tukunyar girki a unguwar Ebute Meta.Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas […]

Ya kashe abokinsa kan tukunyar miya
Ya kashe abokinsa kan tukunyar miya

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan Jihar Legas da ke Yaba sun shiga binciken wani matashi dan shekaru 20 mai suna Ngwuta Nweke kan zargin kashe abokinsa da suke zaune tare a daki daya yayin da suke fada a kan tukunyar girki a unguwar Ebute Meta.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas ta bayyana cewa wanda ake zargi ya shake abokinsa Emeka James yayin da suke kokawa, bayan da musu ya kaure a tsakaninsu a kan tukunyar a ranar Talata.
Ta ce, “A ranar da lamarin ya faru da misalin karfe 12 da rabi na rana, Nweke ya shake James, abokinsa da suke zaune a daki daya a layin Kadara da ke yankin Ebute Meta lokacin da suke fada a kan tukunyar girki. Tuni aka ajiye gawarsa a asibiti sannan ’yan sanda na ci gaba da binciken kan lamarin”.
Nweke ya bayyana wa ’yan sanda  cewa, “James shi ne mai dakin. Na fara zama da shi wata guda ke nan kafin aukuwar lamarin. Ina sayar da famfon mai a kasuwar Idumota, ba ni da kudin da zan kama daki shi ne James ya taimaka mini muke zaune tare. Ranar da lamarin ya auku ina da sauran miya a tukunya sai James ya ce mini in zubar da miyar in ba shi tukunyar zai yi amfani da ita, sai na ce ya yi hakuri in gama amfani da ita, sai ya tashi cikin fushi ya juye miyar a wata tukunya mai datti, sai hakan ya bata mini rai, sai muka fara kokawa, sai na shake masa wuya ta baya, sai muka fadi kasa, sai kawai na ga ya daina numfashi, bayan mun kai shi asibiti sai aka ce ya mutu”.
Makwabtansu sun bayyana James da abokinsa Nweke a matsayin mutane masu hakuri da ba su taba tashin hankali da kowa ba a unguwar.