Ya kashe budurwarsa don ta ki amincewa ta aure shi
Yanzu haka rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame wani matashi dan kimanin shekaru 28, mai suna Raphael Effiong kan zarginsa da kisan budurwarsa mai suna Gift Sunday, mai shekaru 26, saboda ta ki amincewa ta aure shi.Aminiya ta gano cewa ita Gift Sunday, wacce take zaune a kan titin Fadiya a unguwar Ketu tana […]
Yanzu haka rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame wani matashi dan kimanin shekaru 28, mai suna Raphael Effiong kan zarginsa da kisan budurwarsa mai suna Gift Sunday, mai shekaru 26, saboda ta ki amincewa ta aure shi.
Aminiya ta gano cewa ita Gift Sunday, wacce take zaune a kan titin Fadiya a unguwar Ketu tana sana’ar dinki ne, shi kuwa saurayinta Rapheal, dan asalin garin Uyo da ke Jihar Akwa Ibom yana aiki ne da wani kamfanin sadarwa a matsayin direba.
Binciken Aminiya ya gano cewa lamarin ya auku ne a wani otel da aka sakaya sunansa saboda dalilan tsaro da ke unguwar Ketu a karshen makon da ya gabata.
Wani wanda ya shaida yadda lamarin ya auku, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya bayyana cewa Gift da Rapheal sun dade suna soyayya, wacce ta kai har sukan kwana tare a otel.
Majiyar ta ce Rapheal ya dade yana neman budurwarsa Gift ta amince ta aure shi, amma sai ta ce ba za ta aure shi ba saboda shi mutum ne mai wuyar sha’ani.
Majiyar ta ce, “A ranar da lamarin zai auku Rapheal ya kama daki a otel sai ya gayyaci Gift ta kawo masa abinci; da ta kawo abinci sai mamaye ta, ya rika soka mata almakashin da ya boye a tare da shi, har sai da ta fita daga hayyacinta. Kafin a kai ta asibiti ta mutu”.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin shugabannin otel din ya ci tura, saboda daya daga cikin jami’an otel din, wanda ya ki bayyana sunansa, ya ce ba za su ce komai ba saboda lamarin yana wurin ’yan sanda.
Mukaddashin mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Lelma Kolle ta bayyana cewa an samu rashin jituwa tsakanin masoyan, sakamakon haka wanda ake zargi ya yi wa budurwarsa rauni har ta mutu a asibiti.