Ya kashe budurwarsa, ya daka wa kansa wuka

Wani jami’in hukumar kare hadurra ta kasa (FRSC) mai suna Ma’aruf Adamu, da ke zaune a kauyen Chiromawa na karamar hukumar Garun Malam, ya hallaka budurwar da yake nema da aure mai suna Maimuna Chirawa ta hanyar daka mata wuka, sannan shi kuma ya burma wukar a cikinsa, abin da ya kai ga rasuwar Maimuna […]

Ya kashe budurwarsa, ya daka wa kansa wuka

Marigayiya MaimunaWani jami’in hukumar kare hadurra ta kasa (FRSC) mai suna Ma’aruf Adamu, da ke zaune a kauyen Chiromawa na karamar hukumar Garun Malam, ya hallaka budurwar da yake nema da aure mai suna Maimuna Chirawa ta hanyar daka mata wuka, sannan shi kuma ya burma wukar a cikinsa, abin da ya kai ga rasuwar Maimuna nan take, shi kuma ya kai shi ga kwanciya a asibiti.
Wannan al’amarin dai ya faru ne a ranar Talata 17 ga watan Disamba, da misalin karfe 11 na rana. Yayar marigayiya Maimuna, Rahila Musa ta shaida wa Aminiya cewa Ma’aruf ya yi kimanin shekara daya da watanni yana soyayya da kanwarta, kuma dukkansu suna kaunar juna, sai dai ta ce wani abu daya da yake damunta da Ma’aruf shi ne yana dukan Maimuna da zarar ta kata masa rai.
Ta ce, kimanin wata daya da ya gabata ne Ma’aruf ya turo iyayensa daga Daura don tambayar auren Maimuna, inda suka bayar da Naira dubu 10 a matsayin kudin aure suka danka a hannun wani Lawan KT, a matsayin waliyyin Maimuna.
Rahila ta kara da cew,a “da suka kawo kudin, sai na fada musu cewa Ma’aruf yana dukan Maimuna, anya kuwa wannan auren zai yiwu? Da suka fada masa, sai ya ce ai wannan a da ne, daga yanzu ba zai sake dukanta ba. Daga nan sai na tafi Maiduguri na shaida wa Babanmu cewa wani ya kawo kudin auren Maimuna, sai ya ce ta yaya hakan za ta faru bayan ita tana Kirista shi kuma yana Musulmi? Sai na ce da shi Baba ai ta riga ta musulunta. Da ya ji haka sai ya ce ya amince Lawan KT ya zama waliyyin Maimuna wajen maganar aurenta.”
Ta kara da cewa, bayan da ta dawo daga Maiduguri da wani lokaci, sai Maimuna ta kara fada mata cewa har yanzu Ma’aruf yana dukanta. Sai ta ce anya kuwa wannan auren zai yiwu a tsakaninsu? amma kuma ita Maimuna ta dage da cewa tana son sa.
Ta ce bayan wadansu kwanaki, sai Ma’aruf ya kira Maimuna ta waya ya ce mata shi zai karki kudinsa na aure,don ya fasa. Ta ce amma kashegari sai bai je ya karki kudin nasa ba kamar yadda ya fada.
Rahila ta ce a ranar da abin zai faru da safe, Ma’aruf ya hadu da Saratu kanwar Maimuna, sai ya tambaye ta cewa Maimuna tana gida, sai ta ce tana gida tare da Rahila, ba su ma tashi daga barci ba. Ta ce bayan ta fita zuwa wajen aikinta na buga takardu a shagonta ne, tana zaune sai ta ga Maimuna ta je wajenta a goye da Jaririyar da ta dauko daga Barikin ‘Yansanda. Sai ta ce ta je ta mayar da yarinyar ta dawo.
Ta ce, “Ta tafi ta kai yarinyar ke nan sai Ma’aruf ya gan ta, ya bi ta, sannan ya zaro wuka ya daka mata. Dagan an sai ya yi kokarin zai gudu, amma da ya ga ta rike wajen tana kokarin tafiya caji ofis da raunin da ya yi mata, sai ya koma wajenta ya kara soka mata wuka har sau biyu, sai ta fadi ta rasu a nan take. Ni dai ina zaune ina jiran dawowarta, sai kawai na ga ‘yansanda suna kira na suna cewa, ki zo ga Maimuna can ta hadu da Ma’aruf, sai na ce ko dai ya kashe ta ne?” Ta ce daga nan ba ta san sanda ta yanke jiki ta fadi ba, sai ganinta ta yi a kan gadonta bayan ta farfado.
Rahila ta ce, bayan ya soke ta da wukar sai ya yi kokarin tserewa, amma kuma wani Sufeton ‘Yansanda ya gyara bindiga zai harbe shi, da ya ga haka ne sai ya soki cikinsa da wukar, sannan sai ‘yansanda suka kama shi.
Bayanai daga bakin makusantan Ma’aruf sun bayyana cewa ba su san shi da shaye-shayen kayan maye ba, haka nan  kuma babu takin hankali a tare da shi. Wata makwabciyarsa da suke haya a gida daya, Halima Arago ta bayyana cewa, “ni dai abin da na sani shi ne ina ganinsu wata rana tare da budurwarsa suna shigowa gidan, su yi hira tare, amma ban taka ganinsa yana shan wata kwaya ko ma taba ko goro ba.”
A yayin da wakilinmu ya tuntuki babban ofishin hukumar kiyaye hadurra a Kano, Kwamandan Shiyya na hukumar, Muhammad Ibrahim Garba, ya tabbatar da cewa labarin faruwar hakan ta same su. Ya kuma ce, “mu yanzu ba mu da abin yi tun da magana tana hannun  ‘yansanda da hukuma. Da kotu da ‘yansanda su za su yi bincike su tabbatar da faruwar hakan, sannan su yanke hukunci, ba mu ba.”
Ya kara da cewa, idan ma da wani abu da za su yi, sai hukuma ta gama aikinta tukuna, domin wannan abu ne da ya shafi rayuwar shi Ma’aruf ta karan kansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar, Mataimakin sufurtanda Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da faruwar hakan, ya ce a halin da ake ciki Ma’aruf yana wani asibiti mai zaman kansa yana karkar magani, sai ya warke ne za a ci gaba da bincike, tare da gurfanar da shi a gaban kotu don yanke masa hukunci.
Ya kara da cewa, an mika gawar marigayiyar ga ‘yanuwanta. Sai dai kuma yayar marigayiyar ta ce gawar tana hannun hukuma ne, “sai bayan da yayanmu Shettima da kannensa Ibrahim da Yahaya suka roki a bayar da ita sannan aka ce za a bayar da ita a ranar Litinin don yi mata sutura.”
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Ma’aruf a gadonsa na asibiti, bai bayyana masa wani kwakkwaran dalilinsa na halaka marigayiya Maimuna ba, sai dai kawai ya ce tsautsayi ne da kaddara. Ya ce, “komai ba ya faruwa sai da sanin Ubangiji, kuma kaddara ce ta sa ni aikata hakan.” Sannan kuma ya ce yana jiran hukuncin da zai biyo bayan hakan. Sai dai kuma jami’in dansandan da ke tsaronsa a asibitin bai bari a dauki hoton Ma’aruf ba.