Ya ‘kashe’ dan uwansa kan zargin maita

Magidanci ya kashe dan uwansa kan zargin dan uwan na nasa da maita a Jihar Adamawa.

Ya ‘kashe’ dan uwansa kan zargin maita

‘Yan sanda

Wani magidanci ya kashe dan uwansa kan zargin dan uwan na nasa da maita a Jihar Adamawa.

Magidancin mai shekaru 42 ya kashe dan uwan nasa ne a yayin da suke rikici kan zargin da yake cewa wan nasa mai shekaru 57 ya kama kuruwar matar dansa.

Da take gabatar da wanda ake zargi da kisan, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ce wanda ake zargi da kisan ya zargi wansa da sumar da matar dansa ta hanyar maita.

A wani juyin waina kuma, da batun maitar ya bazu a kauyen, sai mutane suka rika kawo marasa lafiyansu ga wanda ake zargin da maita, da sunan neman magani.

Daga baya rikici ya yi tsami tsakanin ’yan uwan junan, har babban ya ce ga garinku nan a sanadiyyar raunukan da ya samu.

Kakakin ’yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje ya ce an tsare wanda ake zargi da kisan domin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.