Ya kashe dan uwansa saboda kaza

Wani matashi mai suna Paul Unegu ya kashe dan uwansa mai suna Sunday Unegu a wata unguwa da ake kira Izzi Unumphu da ke Abakalike, Jihar Ebonyi. Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa cacar baki ce tsakanin wa da kanensa kan kaji ta haddasa lamarin, inda dan uwan yake zarginsa da cewa yana satar […]

Ya kashe dan uwansa saboda kaza
Ya kashe dan uwansa saboda kaza

Wani matashi mai suna Paul Unegu ya kashe dan uwansa mai suna Sunday Unegu a wata unguwa da ake kira Izzi Unumphu da ke Abakalike, Jihar Ebonyi.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa cacar baki ce tsakanin wa da kanensa kan kaji ta haddasa lamarin, inda dan uwan yake zarginsa da cewa yana satar masa kaji.
Matar mamacin ta shaida wa jama’a da suka rika zuwa gidan jajanta mata kan abin da ya faru, cewa mijinta ya dade yana zargin Paul da satar masa kaji duk da jan kunne da yake yi masa amma ya ki, sai ranar ya tafi gidan dan uwan yana zaginsa, don me zai rika dauke masa kaji. Ta ce ita kuma ta yi bakin kokarinta wajen hana shi binsa har gida don su yi fada, amma da yake ajali idan ya yi kira ko b aciwo a je, karshe dai ya fasa kwalba, ya daba wa mijinta. Ta ce an kai shi asibiti amma rai ya yi halinsa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi; ASP George Okafor ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce: “Tabbas bayan lamarin ya kazance har da kisan kai aka sanar da mu. Mai laifin da ake zargi yana hannu, da zarar an gama bincike, kotu za a mika shi.”