Ya kashe dansa kan zargin maita
A Jihar Akwa Ibom wani mutum mai suna Essien Okon ya kashe dansa kan zarginsa dan mai suna Joseph da cewa maye ne. Yadda lamarin ya faru kamar yadda Aminiya ta samu labari shi ne, Okon da matarsa ne suka hada baki suka sanya guba a cikin wani maganin gargajiya da suke kira da Asene suka […]
A Jihar Akwa Ibom wani mutum mai suna Essien Okon ya kashe dansa kan zarginsa dan mai suna Joseph da cewa maye ne.
Yadda lamarin ya faru kamar yadda Aminiya ta samu labari shi ne, Okon da matarsa ne suka hada baki suka sanya guba a cikin wani maganin gargajiya da suke kira da Asene suka tilasta yaron ya sha. Bayan ya sha ne gubar ta ratsa jikinsa ya fita hayyacinsa har ya kai ga mutuwa. Su kuma suka bi dare suka binne shi a cikin daji.
Wata majiya da ke kusa da iyalan Essien Okon mahaifin Joseph ta tabbatar wa Aminiya cewa shi da matarsa ne suka hada baki suka jika maganin mai guba suka ba yaron.
Essien Okon ya shaida wa Aminiya cewa, “Dana maye ne domin shi ne ya kashe matata ta farko da na aura.” Ya kara da cewa bayan mutuwar uwar Joseph ne daga bisani ya auri Peace.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani a ofishinsa, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Akwa Ibom Alhaji Zaki Ahmed ya ce, “Wanda ake zargin ya yi wa jami’anmu bayanin cewa dan nasa maye ne, shi ne ya kashe matarsa ta farko wato uwar yaron ke nan. Shi mahaifin yaron Essien yaudarar yaron ya yi tare da matarsa suka ce masa ya zo su tafi daji satar gwangwala su kawo gida daga nan ne suka ba shi gubar da suka jika masa ya sha ganin ya fita hayyacinsa sai suka kashe shi suka binne shi a can dajin.”
Ya ce ’yan sanda za su gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun gama bincike.