Ya kashe dansa saboda ya dame shi da kukan yunwa
Mazauna layin Fashola da ke unguwar Ejigbo a Jihar Legas sun wayi gari cikin tashin hankali sakamakon zargin da ake yi wa wani dan acaba mai suna Oni Mama da ya kashe dansa mai shekaru uku da duka saboda ya dame shi da kuka kan yana jin yunwa.Aminiya ta gano cewa asirin wanda ake zargi […]
Mazauna layin Fashola da ke unguwar Ejigbo a Jihar Legas sun wayi gari cikin tashin hankali sakamakon zargin da ake yi wa wani dan acaba mai suna Oni Mama da ya kashe dansa mai shekaru uku da duka saboda ya dame shi da kuka kan yana jin yunwa.
Aminiya ta gano cewa asirin wanda ake zargi ya tonu jim kadan da binne gawar dan nasa a yankin unguwarsu a ranar Litinin, makwabtansa suka sanar da ’yan sandan yankin, wadanda suka shiga nemansa, don ya gudu, amma har zuwa hada wannan rahoto ba su same shi ba kuma ba su gano inda ya binne gawar dan nasa ba.
Wani daga cikin makwabtansa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, “Oni ya sha ikirarin zai kashe dansa muddin bai daina yi masa kuka saboda yunwa ba. Yana cewa zai kashe shi kuma babu abin da zai faru. A ranar Litinin ya fito da babur dinsa zai fita aiki, sai yaron ya biyo shi yana kuka yana cewa yana jin yunwa, sai ya kama shi ya shiga da shi cikin daki ya rika duka, daga nan ba mu sake jin kukansa ba, ashe ya kashe shi, sai ya ajiye gawar, sai da dare ya yi ya fita da gawar a cikin buhu duk jini, ya je ya binne, sai daga bisani muka sanar da ’yan sanda”.
Ya ce matar Oni ta rabu da shi watanni da dama da suka gabata, saboda fadansa. “Tun wancan lokaci yaron, wanda bai wuce shekaru uku ba, yake zaune tare da shi. Haka yake ta gararamba a unguwa babu mai kula da shi, ba mai ba shi abinci, ba mai yi masa wanka da wanki, har sai lokacin da mahaifin ya dawo, sannan zai ba shi abin da ya ga dama”, inji shi.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas Ngozi Braide ta wayar salula ya ci tura.