Ya kashe iyayensa da kannensa 2 a Potiskum

Wani saurayi mai suna Adamu Mai-bisco ya kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma kannensa mata biyu a unguwar Batayya a garin Potiskum da ke Jihar Yobe. Adamu dan kimanin shekara 20 da haihuwa ya aikata danyen aikin ne a daren jiya (Litinin) da misalin karfe 11:35 na dare. An sanar da rundunar ’yan sanda, inda […]

Ya kashe iyayensa da kannensa 2 a Potiskum
Ya kashe iyayensa da kannensa 2 a Potiskum

Gawawwakin mamatan lokacin da ake shirin yi musu sallar jana'iza yau (Litinin) a PotiskumWani saurayi mai suna Adamu Mai-bisco ya kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma kannensa mata biyu a unguwar Batayya a garin Potiskum da ke Jihar Yobe.

Adamu dan kimanin shekara 20 da haihuwa ya aikata danyen aikin ne a daren jiya (Litinin) da misalin karfe 11:35 na dare. An sanar da rundunar ’yan sanda, inda suka cafke saurayin nan take.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda a Jihar Yobe, ASP Toyin Gbadegesin ya tabbatar da faruwar al’ammarin. Ya ce wanda ake zargi ya yi amfani da cebur ne wajen kashe mutanen hudu, kuma ya ce ana ci gaba da bincike.

Kodayake, ba a fahimci dalilin kashe-kashen ba tukuna, amma matashin ya shaida wa ’yan sanda cewa gabanin faruwar al’amarin, ya sha maganin “Tramol da kuma tabar wiwi,” kamar yadda ya bayyana.

Sunayen mutanen da ya kashe: Malam Magaji Mai-Bisco mai shekara 65, da mahaifiyarsa mai shekara 50, da kanwarsa Aisha ’yar shekara 16 da kuma Zainab ’yar shekara 14.