Ya kashe kanin mahaifinsa a kan zargin maita
An kama wani matashi dan shekara 24 da ke zaune a kauyan Sabon Birnin Daji da ke a karamar Hukumar Igabi a jahar Kaduna mai suna Sa’idu Iliyasu ana zarginsa da kashe kanin mahaifinsa a bisa zargin maita.Rahotanni daga kauyan sun nuna cewa akasarin mutanen kauyan sun yi mamakin yadda abin ya faru.Da yake bayani […]
An kama wani matashi dan shekara 24 da ke zaune a kauyan Sabon Birnin Daji da ke a karamar Hukumar Igabi a jahar Kaduna mai suna Sa’idu Iliyasu ana zarginsa da kashe kanin mahaifinsa a bisa zargin maita.
Rahotanni daga kauyan sun nuna cewa akasarin mutanen kauyan sun yi mamakin yadda abin ya faru.
Da yake bayani a wurin ‘yan sanda Sa’idu Iliyasu ya ce ya kashe kanin mahaifinsa a gona ne a lokacin da yake shuka, inda ya caka masa wuka a ciki, alhali ya ce babu wata matsala a tsakaninsu. “ Gaskiya babu wata matsala da ta taba hada ni da shi kuma bai yi mun laifin komai ba. Sai dai sun taba yin ‘yar hatsaniya da yayana har ya ce sai ya yi maganinsa. Ni kuma sai na je gonarsa na caka masa wuka a ciki. Bai san ina rike da wuka ba lokacin da na je. Kuma na kashe shi ne saboda mutanen garin suna zarginsa da maita,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko ya yake ji a yanzu? sai ya ce, “ Ba na jin dadi a raina, saboda ni ban san abin da ya sa na je na kashe shi ba, amma dai kaddara ce daga Allah.”
Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan Sandan Jahar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya tabbatar da faruwar al’amarin kuma ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su kai wanda ake zargin kotu.
A wata sabuwa kuma rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna ta yi nasarar kama wadansu ‘yan damfara su shida wadanda suka yi kaurin suna wajen cutar jama’ar jahar.
daya daga cikinsu mai suna Obiora ya bayyana wa manema labarai cewa daga Abuja ya zo Kaduna domin aiwatar da wannan sana’a munmunar tasa.
“ Muna zaune Abuja ne daga baya sai na dawo Kaduna a bisa gayyatar abokan aikina. Kuma a gaskiya babu wani dadi a wannan sana’a sai wahala, saboda ni har yanzu ban samu wani kudin a-zo-a-gani ba,” inji shi.
‘Yan sandan sun same su da lambobin wayoyin mutane da yawa a hannunsu wanda suke amfani da su wajen kiran mutane suna masu karya da nufin danfararsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Aminu Lawan ya shawarci mutane su yi hattara da irin wadannan mayaudara. Domin sun taba kama su a wadansu lokuta a baya sun kuma kai su kotu. “ Za mu tabbatar sun dauki lokaci mai tsawo a gidan Yari saboda sun dade suna cutar mutane, musamman a kan hanyar da ta bi bayan gari (Bypass) watau titin Nnamdi Azekwe zuwa wuraren Kudenda da Nasarawa,” inji shi.