Ya kashe kansa da ’ya’yansa 2 don an kore shi daga aiki
Wani uba ya kashe ’ya’yansa biyu kafin daga bisani ya harbi kansa da bindiga domin an sallame shi daga aiki, kamar yadda jaridar Daily Mail ta bayyana.Mutumin mai suna, Julian Roary, mai shekara 47 da haihuwa, wanda shi ne mahaifin ’ya’yan biyu: guda dan shekara 10, guda kuma dan shekara 12, ya aikata wannan danyen […]
Wani uba ya kashe ’ya’yansa biyu kafin daga bisani ya harbi kansa da bindiga domin an sallame shi daga aiki, kamar yadda jaridar Daily Mail ta bayyana.
Mutumin mai suna, Julian Roary, mai shekara 47 da haihuwa, wanda shi ne mahaifin ’ya’yan biyu: guda dan shekara 10, guda kuma dan shekara 12, ya aikata wannan danyen aikin ne a gidansa da ke garin Baltimore na kasar Amurka.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ya ce Mista Julian yana cikin wani yanayi ne bayan da ya rasa aikinsa kuma bai kai ga samun wani abin yi ba, a daidai lokacin da al’amarin ya faru. Kodayake, an ce bai bayyana dalilin da ya sa shi yin hakan ba a wasiyyar da ya bari.
Mista Julian da babban dansa a nan take dai suka rasu, amma karamin dansa sai bayan da aka kai shi asibiti ne ya cika.
Bazawarar marigayin ta bayyana yaran da wadanda kowa zai yi alfahari da su. Ta ce tun da babansu ya rasa aikinsa a shekarar 2009 ya shiga cikin wani mawuyacin hali. “A kullum yakan shiga damuwa sosai idan matsalolin kudi musamman na sauke nauyin iyalinsa suka bijiro masa,” inji ta.