Ya kashe kansa kan tilasta masa komawa Arewa
Wani mutum mai suna Muhammad Sani Kafinta da ke zaune a kasuwar Mil 12 a Legas, mai kimanin shekaru 50, ya rataye kansa kan an tilasta masa ya ziyarci garinsu a Jihar Sakkwato.Wani abokin huldarsa mai suna Haruna Wanzan ya shaida wa Aminiya, a karshen makon da ya gabata, cewa Muhammad Sani, wanda ake wa […]

Wani mutum mai suna Muhammad Sani Kafinta da ke zaune a kasuwar Mil 12 a Legas, mai kimanin shekaru 50, ya rataye kansa kan an tilasta masa ya ziyarci garinsu a Jihar Sakkwato.
Wani abokin huldarsa mai suna Haruna Wanzan ya shaida wa Aminiya, a karshen makon da ya gabata, cewa Muhammad Sani, wanda ake wa lakabi da Sani Kafinta ya shafe kimanin shekaru 27 bai je gida ba.
Ya ce, “An ce Sani bai taba zuwa gida ba cikin shekaru 27. Mahaifiyarsa ce ta turo a tafi da shi. Lokacin da ’yan uwansa suka zo don su tafi da shi, misalin sallar Asuba ranar Juma’a, sai ya shiga cikin dakinsa ya rataye kansa, ya mutu. Mun yi mamaki, domin ni a sanina da Sani, ban taba zaton zai yi haka ba, saboda mutum ne mai hakuri, wanda ba ya son tashin hankali. Ba mu taba jin ya yi hayaniya da wani ba. Komai dare idan ka tashe shi ka ce ya yi maka aiki zai yi ba tare da wata matsala ba”.
Makwabcinsa kuma abokinsa mai suna Umar Usman ya ce, “Mutuwar Sani ta yi harshen damo. Wasu na cewa ya kashe kansa ne a lokacin da aka zo za a tafi da shi gida shi kuma ba ya son tafiya. Wasu kuma suna cewa ya kashe kansa ne saboda tabin hankalin da ya gamu da shi ’yan kwanaki kafin haka, amma ni na fi yarda da tabin hankalin da ya gamu da shi domin kafin mutuwarsa ya yi ta nuna halayyar surutai barkatai. Za ka ji yana cewa ga sojoji sun zo za su kashe shi. Ni ina ganin ba yadda za a yi mai hankali ya rataye kansa.
“Mun dade tare da shi a nan kasuwar, amma ba mu taba ganin ya je gida ba kuma bai taba gaya mana cewa yana da iyali ba, amma idan ana hira wasu sukan zolaye shi cewa ba ya zuwa gida, amma sai ya rika cewa ba ruwansu, idan zai je gida ba sai ya gaya wa jama’a ba. Shi mutum ne mai hakuri, ba ya fada. Shi ya sa a lokacin da ya rataye kansa mun yi mamaki kwarai, ba mu taba zaton zai yi haka ba”. Inji shi.
Mutane da dama da Aminiya ta tattauna da su a kasuwar sun bayyana Sani Kafinta a matsayin mutumin arziki, wanda yake neman na kansa.
Mataimakin shugaban kasuwar Mil 12, Alhaji Sahabi Sakkwato ya bayyana bakin cikinsa da faruwar lamarin. “Gaskiya lokacin da abin ya faru ba mu ji dadi ba, mun yi bakin ciki kwarai. Saboda haka muna kira ga mutanenmu su guji aikata irin wannan mummunan laifi”. Inji shi.
Wani malami mai suna Sama’ila dalhatu ya bayyana cewa, “Manzon Allah ya ce duk musulmin da ya kashe kansa to ranar lahira za a yi masa azaba da abin da ya kashe kansa da shi. Saboda haka wannan mutum ya aikata babban laifi, amma bai fita daga da’irar Musulunci ba”.
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce ba ta da labarin aukuwar lamarin, sai dai za ta bincika don gano gaskiyar abin da ya auku.