‘Ya kashe kansa ne saboda an zarge shi da lalata’

Dangin wani gwanin girki dan asalin kasar Japan wanda ke tashe a Faransa, Taku Sekine, sun ce ya kashe kansa ne saboda an zarge shi da aikata fyade. “An kaddamar da wani mugun kamfe ne don tarwatsa rayuwarshi”, a cewar dangin a wata sanarwa da suka aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta maraicen […]

‘Ya kashe kansa ne saboda an zarge shi da lalata’

Iyalin Taku Sekine sun ce ya kashe kansa ne saboda an sako shi gaba a kafofin sadarwa na zamani (Hoto: Femme Actuelle)

Dangin wani gwanin girki dan asalin kasar Japan wanda ke tashe a Faransa, Taku Sekine, sun ce ya kashe kansa ne saboda an zarge shi da aikata fyade.

“An kaddamar da wani mugun kamfe ne don tarwatsa rayuwarshi”, a cewar dangin a wata sanarwa da suka aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta maraicen Talata.

A 2016 ne mujallar abinci ta Fooding ta ayyana dan karamin gidan sayar da abinci na mutumin mai suna Dersou da cewa ya fi ko wanne iya girki a Faransa.

Sai dai a cewar dangin nasa, Sekine, mai shekara 39 da haihuwa, ya afka cikin wani yanayi na “mummunar damuwa” bayan an sako shi gaba “da yada karairayi da tsegunguma” a kafofin sadarwa na zamani a watanni biyu da suka gabata.

‘Babu korafi’

Sun kara da cewa hakan wani yuknkuri ne na dakushe martabar da yake da ita a tsakanin abokan aikinsa wadanda aka yiwa gargadin su guji aiki tare da shi.

Dangin sun kuma yi Allah-wadai da abin da suka ce wani shafin intanet na abinci – wanda bas u ambaci sunanshi ba – ya yi wa Sekine.

Sun kara da cewa babu wani korafi da aka kai wa hukumomi game da gwanin girkin, kuma ’yan sand aba sa bincike a kan shi.

A watan Agusta dai shafin intanet na Atabula ya wallafa wani dogon bincike game da fyade da lalata da ake aikatawa a gidajen sayar da abinci na Faransa, yana cewa “za a iya zargin wani gwanin girki dan asalin Japan”, wanda bai bayyana sunansa ba, “da aikata fyade”.

An dade ana ruwa

Ranar Talata, sa’o’i kadan bayan Sekine ya kashe kansa, shafin ya ambato wata mata tana ikirari cewa wani fitaccen gwanin girki, Guy Martin, ya yi yunkurin yi mata fyade.

A cewar matar mai suna Florence Chatelet Sanchez, wacce ke samar da kayan abinci ga manyan gidajen abinci na Faransa, Mista Martin ya matse ta a jikin bango a daya daga cikin gidajen abincinsa ya kuma yi yunkurin tube ta shekaru biyar da suka wuce.

Daga bisani fitaccen gwanin girkin ya musanta zargin, yana cewa ba shi da tushe bare makama.

Ranar Laraba shafin Atabula ya wallafa hujjar binciken da ya yi a kan fyade da lalata a harkar sayar da abinci yana mai cewa majiyoyi da dama sun ambaci sunan Sekine a lokuta daban-daban idan ana maganar (yunkurin) tursasa mata.

A cewar shafin, a watan Agusta wata ’yar Canada mai shekara 25 a duniya ta yi ikirari a shafin Isntagram cewa sau biyu yana yunkurin afka mata lokacin da take barci a watan Janairun 2019.

“Iyaye da dama wadanda ’ya’yansu suka yi aiki a gidajen sayar da abinci sun yi mana godiya saboda tabo wannan batu da muka yi bayan ’yan’yansu maza da mata wadanda ba za su iya furta komai game da ukubar da suka fuskanta ba sun hallaka kansu”, a cewar marubucin labarin kuma jagoran binciken, Franck Pinay-Rabaroust.

Masana dai sun yi gargadin cewa abubuwa da dama da matsalolin kwakwalwa wadanda za a iya magancewa kan taka rawa wajen ingiza mutane su kashe kansu.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo