Ya kashe kansa kan zargin matarsa na lalata da abokansa

Wani magidanci mai ’ya’ya uku ya rataye kansa bisa zargin matarsa da bin maza a Jihar Nasarawa.

Ya kashe kansa kan zargin matarsa na lalata da abokansa

Wani magidanci mai ’ya’ya uku ya rataye kansa bisa zargin matarsa da cin maza a yankin Masaƙa da ke Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Kakakin ’yan sandan jihar,  DSP Nansel Ramhan, ya shaida mana a ranar Laraba cewa a safiyar Litinin aka tsinci gawar mutumin a rataye a cikin aji a Makarantar Crystal da ke Masaƙa.

Ya ce wani malamin makarantar ne ya kawo rahoto cewa an ga wani baƙon mutum an rataye ta a jikin silin ɗin ajin.

“Bayan samun rahoton ne DPO da jami’ansa suka je suka kai shi Babban Asibitin Mararaba, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu, aka ajiye gawar a mutuware,” in ji DSP Ramhan.

Ya ce babu wata takarda ko saƙo da mamacin ya bari, amma rundunar tana bincike don gano musabbabin mutuwar.

Game da zargin cin amanar auren da matar mutumin ke yi ne ya sa shi kashe kansa, jami’in ya ce ba shi da masaniya, amma suna bincike.

Amma wani sako da wakilinmu ya yi karo da shi a Facebook ya yi iƙirarin cewa magidancin ya  hallaka kansa ne bayan da ya gano cewa abokansa suna kwana da matarsa suna ba ta kuɗi.

Sakon ya yi iƙirarin cewa ko da mutumin ya tunkari matar, sai ta shaida masa cewa tana lalata da su ne saboda shi ya kasa daukar dawainiyar ciyar da iyalisa.

A cewar sakon, matar ta shaida wa mijin nata mai shekaru 38 cewa da kuɗin da ake biyan ta take ciyar da kanta da shi da ’ya’yansu uku.

Mutum 14 sun rasu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a Taraba

’Yan bindiga sun harbi likita, sun sace mutum 5 a asibiti a Katsina

Manoma 7 sun rasu a hatsarin mota a Minna

Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN