Ya kashe kawunsa kan zargin maita a Adamawa
Wani mutum ya kashe kawunsa kan zargin maita a yankin Dumna Zarbu da ke Karamar Hukumar Guyuk ta Jihar Adamawa.
Wani mutum ya kashe kawunsa kan zargin maita a yankin Dumna Zarbu da ke Karamar Hukumar Guyuk ta Jihar Adamawa.
Wanda ake zargin mai shekaru 42 dai ya musanta aikata laifin da aka gurfanar da shi a kai.
Shaida sun ce mamacin ya rasu ne bayan dan nasa ya buge shi da sanda saboda an zarge shi ne da kisan wasu mutane ta hanyar maita, zargin da ya musanta.
Bayan sauraron karar ne alkali Alheri Ishaku ta babbar kotun majistare ta daya da ke Yola ta ba da umarnin tsare wanda ake zargi da kisan a gidan yari.
- Kotu ta ci tarar gwamnan Kano N25m kan zargin Alhassan Doguwa da kisa
- Ma’aikatun da suka fi samun kudi a kasafin 2024
Daga nan ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024.