Ya kashe mahaifinsa da mutum 9 a masallaci

Da Asubahin shekaranjiya Laraba ce wani dan kunar bakin wake ya kutsa kai cikin wani masallaci a Jihar Borno inda ya ta da bam din da ya sanadiyar kashe kansa da sauran mutum tara ciki har da mahaifinsa, sannan ya raunata wadansu da dama. Maharin, wanda aka hakkake dan Boko Haram ne, ya kutsa kai […]

Ya kashe mahaifinsa da mutum 9 a masallaci

Da Asubahin shekaranjiya Laraba ce wani dan kunar bakin wake ya kutsa kai cikin wani masallaci a Jihar Borno inda ya ta da bam din da ya sanadiyar kashe kansa da sauran mutum tara ciki har da mahaifinsa, sannan ya raunata wadansu da dama.

Maharin, wanda aka hakkake dan Boko Haram ne, ya kutsa kai cikin masallacin ne da ke kusa da gidan mahaifinsa a Unguwar Abuja da ke garin Gamboru da nufin hallaka masallatan. 

“Da misalin karfe biyar na Asubahi, ina kan hanyata ta zuwa masallaci sai na ji karar fashewar bam daga masallacin da nake nufin zuwa. Nan take na tsaya, na dawo gida. Bayan komai ya lafa, na koma wurin tare da sauran mutane, inda muka zakulo wadanda suka ji rauni, tare da ciro gawarwaki  goma,” inji Muhammadu Mustapha.

Haka shi ma wani da ya tsira daga harin, mai suna Sheriff Abba, ya ce dan ta’addar ya dade cikin masallacin kafin mutane su fara zuwa.