Ya kashe mahaifinsa kan karan sigari
’Yan sanda a Jihar Edo sun kama wani matashi mai kimanin shekara 25 mai suna Bestman Momodu bisa zargin kashe mahaifinsa mai suna Zubeiru Momodu ta hanyar daba masa wuka kan karar sigarin Naira 10.Lamarin ya auku ne a kauyen Ubiane da ke yankin Abiele a karamar Hukumar Estako ta Yamma da ke Jihar Edo […]
’Yan sanda a Jihar Edo sun kama wani matashi mai kimanin shekara 25 mai suna Bestman Momodu bisa zargin kashe mahaifinsa mai suna Zubeiru Momodu ta hanyar daba masa wuka kan karar sigarin Naira 10.
Lamarin ya auku ne a kauyen Ubiane da ke yankin Abiele a karamar Hukumar Estako ta Yamma da ke Jihar Edo a ranar 16 ga Agustan da ya gabata, kamar yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Foluso Adebanjo ya bayyana.
Bestman, wanda dan asalin karamar Hukumar Etsako ta Yamma ne, kuma ya furta cewa ya aikata laifin ya ce, ya shanye tabar ta mahaifinsa ne, inda takaddama ta kaure a tsakaninsu lokacin da mahaifinsa ya gano sigarinsa ta bace.
Wanda ake zargin ya ce lokacin da takkadama ta yi zafi a tsakaninsa da mahaifinsa ne ya fito da wuka ya daba wa mahaifin nasa sau uku inda ya kashe shi nan take.
Wanda ake zargin ya ce: “Na saci sigarinsa ne, kuma lokacin da ya gano, sai ya farad aka min tsawa yana nemana da rigima. Bisa kuskure ni kuma sai na dauko wuka na daba masa. Ban ga gawarsa ba, amma na ji labarin ya mutu. Kuma mutanen kauyen ne suka kama ni bayan na kashe shi. Kun san irin rayuwar da muke gudanarwa, kuskure ne.”
Bestman yana daga cikin mutum 68 da Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo ta gabatar a hedkwatarta a ranar Litinin da ta gabata, da ake zargi kan laifuffuka daban-daban da suka hada da fyade da fashi da makami da kisan kai da satar mutane da mallakar makami ba bisa ka’ida ba da sauransu.
Kwamishina Foluso Adebanjo ya fadi lokacin gabatar da wadanda ake zargin cewa, ya kamata mazauna jihar su rika lura musamman a daidai lokacin da muke tunkarar karshen shekara lokacin da ayyukan miyagu suke karuwa.
Idan za a iya tunawa a watan Yuli da ya gabata, wani dalibi dan shekara 21 mai suna Tolani Ajayi na Jami’ar Redeemers Unibersity ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan ya yanka mahaifinsa mai shekara 60, mai suna Mista Charles Ajayi, wani Babban Lauya a Najeriya (SAN) a ranar 3 ga Yuli, inda ya sanya gawarsa a cikin akwatu ya jefar.