Ya Kashe Mahaifinsa Kan Kyautar Fili

Wani dattijo ya bakunci lahira bayan dansa ya sossoka masa wuka saboda ya ki ba shi kyautar fili.

Ya Kashe Mahaifinsa Kan Kyautar Fili

Gawa

Wani matashi ya soka wa mahaifinsa wuka har lahira saboda mahaifin ya ki ba shi kyautar fili.

Matashin ya yi aika mahaifin nasa barzahu ne saboda mahaifin ya bukaci ya ba shi lokaci ya kasafta filin yadda zai yi wa sauran iyalansa adalci.

Matar marigayin ta ce: “Ya dade yana damun mijina shekara guda ke nan kan filin nan.

“A ranar Litinin ne maganar ta kai su ga musayar yawu, inda ya fusata ya zaro wuka ya sossoka wa mahaifin nasa a kai da wuya da hannaye da kafafunsa har ya mutu.

“Ihun da na yi ne bayan ganin abin da ya faru ya sanya ya tsere”, in ji ta.

A safiyar ranar Litinin ne al’ummar unguwar Masaka a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa suka wayi gari da wannan danyen aiki na kisan magidancin da dansa ya yi.

Kanin wanda ake zargi da aikata ta’asar, kuma da na biyu ga margayin ya ce sun sanar da ’yan sanda, gawar mahaifin nasu kuma na ke ajiye a mutuware kafin kammala bincike.