Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi shaye-shaye 01

Wani matashi mai shekara 25 mai suna Bello Malami ya kashe mahaifinsa Malami Aliyu mai shekara 56 a ranar Lahadin da ta gabata a Unguwar kofar Rini da ke Sakkwato, saboda ya hana shi shaye-shaye.Mahaifiyar matashin Malama Fatima Malami ta shaida wa Aminiya cewa “A ranar Lahadi da misalin karfe 2:00 na dare ina kwance […]

Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi shaye-shaye 01
Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi shaye-shaye 01

Wani matashi mai shekara 25 mai suna Bello Malami ya kashe mahaifinsa Malami Aliyu mai shekara 56 a ranar Lahadin da ta gabata a Unguwar kofar Rini da ke Sakkwato, saboda ya hana shi shaye-shaye.
Mahaifiyar matashin Malama Fatima Malami ta shaida wa Aminiya cewa “A ranar Lahadi da misalin karfe 2:00 na dare ina kwance a waje kusa da dakin mahaifinsa sai Bello ya shigo rike da adda ya nufi marigayin, sai na ce sara masa adda za ka yi sai ya ce sai na kashe shi nan take sai ya buga masa ita a kai lokacin yana sallar nafila ta dare kuwwarsa ke da wuya sai yaron ya  biyo ni na shige dakina na kulle ina jin mahaifin na neman agaji amma ban fito ba gudun kada ni ma ya hallaka ni. ”
Ta ce shi ne babban dansa sai kanensa da kuma juna biyun da take dauke da shi. “Da safiyar Litinin na saci jiki, na fita na sanar da makwabtana abin da ke faruwa suka zo domin bincikar lamarin. Ban san da wata jikakka a tsakaninsa da mahaifinsa ba,” ta fadi cikin kuka.
kane kuma makwabcin marigayin mai suna Buhari Abubakar More da ke cikin wadanda suka kai agaji da safe, ya ce wasu na zargin yaron ya kashe mahaifinsa ne don ya hana shi shaye-shayen miyagun kwayoyi da shalinsho.
Ya ce lokacin da suka je gidan sun iske yaron a tsaye bakin kofa rike da sabuwar adda yana cewa ba wanda zai shiga gidansu. “Da na yi kokarin shiga sai ya sare ni a hannu, da muka fi karfinsa muka shiga gidan, muna isa bakin dakin marigayin sai muka ga wani dogon rami muka kira ’yan sanda suka zo aka tone ramin sai ga gawar marigayin an sassare ta ko’ina an cire hanci da lebbansa,” inji Buhari.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato DSP Almustafa Sani shi ne ya tabbatar wa Aminiya cewa matashin yana hannunsu kuma da zarar sun kammala bincike za su kai shi kotu.