Ya kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya

Dan uwan mahaifin yaron ya ce dama yana shaye-shaye

Ya kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya

Gawa

Wani matashi mai suna Kazeem Muhammad ya tsere bayan kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya shekara daya da ta gabata a garin Suleja da ke jihar Neja.

Dan uwan marigayin mai suna Isah ya shaida wa Aminiya cewa bayan ya kwada wa mahifin nasa falanki a ka, take Kazeem ya cika wandonsa da iska.

Ya ce, “Matashin na shaye-shaye sosai, don haka ya saba aikata abubuwan da ba su kamata ba.

“Ranar Laraba da safe ne sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da mahifin nasa, sai ya kwada masa wani falankin katako da ke gurin, kuma take ya fadi, shi kuma ganin haka sai ya tsere.

“Mun kai shi asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma a nan take ya ce ga garinku nan,” inji dan uwan marigayin.

Ya kuma ce tuni suka sanar da hukumomin da suka kamata domin daukar mataki, sannan suka binne gawar mamacin.

Sai dai Rundunar ’Yan Sandan yankin ta ki cewa uffan a kan lamarin.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi