Ya kashe mahaifinsa, ya binne shi a gidansu
Matashin ya ce ya ɗauki matakin ne saboda mahaifin nasa ya tsane shi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja, ta kama wani matashi mai shekara 29 mai kan zargin kashe mahaifinsa mai shekara 65 a duniya.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Waisu Abiodun ne, ya bayyana hakan a Minna a ranar Talata, inda ya ce an kai rahoton faruwar lamarin ofishin ’yan sanda da ke Kpakungu.
- EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON kan aikin Hajjin 2024
- Dambaruwar NIN: MTN ya kulle dukkanin ofishinsa a Najeriya
Ya ce, “A ranar Talata da misalin ƙarfe 10 na safe ne aka samu labari a ofishin da ke Kpakungu cewa ranar Litinin wani Abubakar Adawa ya ɓace a unguwar Barkin-Sale a Minna.”
Abiodun ya ce jami’an ’yan sandan da ke aiki a sashen ƙarƙashin jagorancin jami’in ’yan sanda na yankin sun ziyarci gidan wani dan shekara 29 suka yi masa tambayoyi tare da mahaifiyarsa, da ke zaune tare da shi a gidan.
Ya ce, “An yi bincike sosai a gidan baki ɗaya, kuma abin mamaki, an gano gawar wanda ya ɓace a cikin wani rami mara zurfi a gidan.”
Abiodun, ya ce matashin ya amsa laifin kashe mahaifinsa ne saboda ya tsane shi.
Kakakin ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi amfani da fartanya ne wajen kashe mahaifin nasa, sannan ya binne shi a wani rami.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kafin miƙa wanda ake zargin a kotu.