Ya kashe mahaifiyarsa da kannensa saboda kudi

A makon jiya ne mutanen garin Gusau, musamman mazauna unguwar nan da ake kira Mutuwa Geji, suka wayi gari cikin tashin hankali da tsoro da kuma mamaki, a lokacin da suka samu labarin cewa wani matashi mai suna Kamalu Yusif ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar yi mata yankan Rago tare da wadansu abokansa, ya kuma […]

Ya kashe mahaifiyarsa da kannensa saboda kudi
Ya kashe mahaifiyarsa da kannensa saboda kudi

A makon jiya ne mutanen garin Gusau, musamman mazauna unguwar nan da ake kira Mutuwa Geji, suka wayi gari cikin tashin hankali da tsoro da kuma mamaki, a lokacin da suka samu labarin cewa wani matashi mai suna Kamalu Yusif ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar yi mata yankan Rago tare da wadansu abokansa, ya kuma hada da kannansa guda biyu.
Yadda abin ya faru kuwa shi ne, Kamalu, wanda aka ce dangata ne, don babu abin da ya rasa a rayuwa, don har motar hawa an saya masa kuma an dauki nauyin karatunsa,  amma duk wannan bai yi masa ba.
Hajiya Hafsatu ita ce mahaifiya Kamalu wanda ta haifa da wani kafin ta auri wani aattajiri amma sai Allah Ya yi masa rasuwa, bayan rasuwarsa sai aka ba ta kasonta na gado, da yake kuma sun samu haihuwa da shi marigayin.
Kamalu ya sanya idanu matuka kan wannan dukiya da ya ga mahaifiyarsa tana da shi, don haka sai ya dauka  ai shi ma yana da gado, hakan ya sa ya rika  yi mata barazanar  kisa, kai ba ma ita kadai ba har da wadansu kawunensa da yayyinsa.
Abinka da karar kwana, Hajiya sai ta dauki Kamalu ranar Jumu’a suka je wani banki suka karbo kudi har Naira dubu dari takwai, cikin wannan kudin ne Kamalu ya bukaci Hajiya ta ba shi wani abu, amma ta ki yarda, wannan ya sa Kamalu ya tafi ya shirya da wadansu abokansa suka zo cikin dare suka yi mata yankan rago, suka kuma dauki sauran kannansa aka yi wa daya yankan rago, daya kuma ana zargin wuyanta aka murde.
Kamalu sai ya dauki motar da mahaifiyarsa take amfani da ita da kuma wannan kudi Naira dubu dari takwas  ya gudu Kaduna.Sai aka samu nasarar kama shi. Kuma wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewa an samu wadansu kudin tare da shi da suka kai Naira dubu dari biyar.
Amina, wadda aka fi sani da suna Mommy, da ba ta wuce shekara goma sha hudu ba da kuma kanwarta mai suna Maryam, da ba ta wuce shekara goma ba, sune kannen Kamalu da ake zargin ya kashe su, ya dauki gawarwakinsu ya jefa cikin ruwa, sai daga baya aka samu nasarar tsamo su  aka yi musu jana’iza.
Wata majiya ta sheda wa wakilinmu cewa, mahaifiyar Kamalu ta sanya shi a makarantar Polytechnic  da ke Bauchi, da ba ta gamsu ba sai ta koma da shi Jami’ar Al-hikmah  da ke Ilorin, da ta ga bai natsu ba sai ta dawo da shi kusa da ita, ta sanya shi makarantar Abdu Gusau yana karanta fannin kwamfuta, domin a wadansu lokutta a baya sai da ta je ta biya wadansu wayoyi da kwamfutoci da ya sato .
Mahaifiyar wannan yaro ta jima tana fuskantar barazanar kisa daga gare shi ,kuma ta sha fada wa mahaifinsa (wato tsohon mijinta) wannan matsala, amma abin ya zam a sai dai addu’a.
A halin da ake ciki yanzu dai Kamalu  yana hannun ‘yansanda suna gudanar da bincike kafin su kai shi gaban kuliya.
DSP Lawal Abdullahi shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar  ‘yansanr Jihar Zamfara, Aminiya ta nemi jin ta bakinsa amma wayarsa a kashe take.