Ya kashe mahaifiyarsa don ta hana shi yawon dare
‘Yan sandan sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Iyaganku a birnin Ibadan, a karkashin ACP Dasuki Galadanci, sun kama matashin da ya halaka mahaifiyarsa, ta hanyar sara da adda, inda suka gurfanar da shi gaban kotun majastare a Larabar makon jiya. Bayan an karanta tuhumar kisan kai da aka yi wa mai laifin alkalin […]
‘Yan sandan sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Iyaganku a birnin Ibadan, a karkashin ACP Dasuki Galadanci, sun kama matashin da ya halaka mahaifiyarsa, ta hanyar sara da adda, inda suka gurfanar da shi gaban kotun majastare a Larabar makon jiya. Bayan an karanta tuhumar kisan kai da aka yi wa mai laifin alkalin kotun mai shari’a Omotosho ya bayar da umarnin a tsare kadri a gidan yari har zuwa ranar 6 ga watan Oktoba inda aka aka ci gaba da sauraron karar.
Tun a watan Satumbar da ya wuce ne, wani matashi ya dauko wata adda ya kama saran mahaifiyarsa, inda ya yi sanadin mutuwarta a cikin gidansu da ke kauyen Temidire Oloso, cikin karamar hukumar Surulere a Jihar Oyo. Wannan al’amari ya auku ne saboda tsohuwa Afusat Amope, mahaifiyar matashin ta tsare danta kadir Yusuf, a cikin gida ta ja masa kunne, kan ya daina yawon dare, tare da yi masa addu’o’in neman kariya daga dukkan abin da zai cuce shi, amma wannan nasiha ba ta shiga kunnensa ba, a maimakon haka ma fusata ya yi ya kama cin zarafin mahaifiyar tasa da ikirarin daina taimakon da ya saba yi mata wanda a karshe dai ya halakata.
Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa wakilinmu cewa, marigayiya Afusat, tana yawan jan kunnen dan nata ya daina yawon dare ne, saboda tana tsoron kada ya fada hannun matsafa da ‘yan fashi da makami, amma sai ya yi kunnen kashi da nasihar tata.
Kafin a kai ga gurfanar da kadri mai shekaru 30 da haihuwa gaban kotu, wakilinmu ya samu tattauna wa da shi a wurin da yake tsare a hannun ‘yan sanda. Da farko ya fara da nuna nadamar abin da ya aikata, har ya nemi gwamnatin kasa ta yafe masa, domin a cewarsa bai san abin da ya ingiza shi har ya kashe mahaifiyarsa ba. Da yake amsa wata tambaya, ya fara nokewa ne daga baya ya amince da zukar tabar wiwi da wasu abubuwan sanya maye kafin ya aikata danyen aikin nasa.
Ya ce da shi da mahaifiyarsa sun fita daga cikin gidan nasu zuwa wasu wurare daban –daban. Da ya riga ta dawowa, sai ya shige cikin daki tare da matarsa, daga baya da ya gano mahaifiyar ta dawo, sai kawai ya nemo adda ya shiga dakinta ya kama saranta. A firgice ta tashi ta ruga zuwa cikin dakinsa, domin neman taimakon shi, saboda ba ta san cewa shi ne yake biye da ita ba. A lokacin da yake kokarin gudu ne ya taka kafar matarsa da ta farka daga barci ta fara kururuwa da ta jawo makwabta suka kama shi.
Majiyar ta ce, mazauna kauyen sun yi tir da aukuwar wannan al’amari, inda suka lashi takobin ganin ba za su kyale wannan matashi ya sake dawowa cikinsu ba. A cewarsu duk mutumin da zai iya kashe mahaifiyarsa to, kuwa ba abokin zama cikin jama’a ba ne.