Ya kashe mai ciki don yin tsafi da mahaifarta
Matashi dan shekara 28 a duniya, Mista Edet Stephen Asukuo ya tona wa kansa asiri, inda ya gaya wa ’yan sanda a Akwa-Ibom cewa wani shugaban al’umma ne ya dauke su haya bisa ijarar Naira dubu 50, cewa ya kashe wata mata mai ciki, domin amfani da mahaifarta wajen yin tsafi.Shi dai wanda ake zargi […]
Matashi dan shekara 28 a duniya, Mista Edet Stephen Asukuo ya tona wa kansa asiri, inda ya gaya wa ’yan sanda a Akwa-Ibom cewa wani shugaban al’umma ne ya dauke su haya bisa ijarar Naira dubu 50, cewa ya kashe wata mata mai ciki, domin amfani da mahaifarta wajen yin tsafi.
Shi dai wanda ake zargi da kashe matar mai ciki, ’yan sanda sun kama shi ne a makon jiya, bayan da ’yan uwansa suka kai rahotonsa a ofishin ’yan sanda. Bincike ya tabbatar da cewa, an samu gawar matar ce a wata gona da ke kusa da gari.
A lokacin da ’yan sanda suke gabatar da wanda ake zargin gaban manema labarai a hedikwatarsu da ke Ikot-Akpanabia, Jami’ar hulda da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar, Cordelia Nwawe ta ce: “Babu wani mutum da ke da ikon kashe wani mutum, ba wanda zai lamunce masa haka. Wannan abin da ya aikata, ya nuna cewa ya kashe matar nan kuma ya kashe dan tayin da ke cikinta.”
Jami’ar ta ce, shi wanda ake zargin, dama can ya san matar, kasancewar yana yin sayayyar kaya a wurinta. Shi ne ya bi ta har zuwa shagonta da ke kasuwa da nufin zai yi sayayya daga wurinta kamar yadda ya saba. Daga bisani kuma sai ya kara bin ta zuwa gidanta, da cewa yana da bukatar karin sayen hajar tata. “Sai dai maimakon ya sayi kayan nata sai ya kashe ta kuma ya boye gawarta da nufin cire mahaifarta domin yin tsafi da ita.” Inji jami’ar ta ’yan sanda.
’Jami’ar ’yan sandan ta ce ’yar uwar wanda ake zargi da kisan ce ta ga lokacin da dan uwan nata yake aikata kisan matar, domin haka ta kai rahotonsa zuwa ga ’yan sanda. Amma a lokacin da yake bayyana yadda al’amarin ya faru ga manema labarai, wanda ake zargin mai suna Edet Stephen ya ce: “Abin da ya sanya aka kawo ni ofishin ’yan sanda shi ne, saboda wani aiki da na yi. Wani shugaban al’umma ne ya dauke mu haya, mu biyar, ya ce zai biya mu domin mu kashe matar mai ciki, mu kai masa kanta da kuma mahaifarta mai dauke da dan tayi, domin ya yi amfani da shi wajen tsafi, da nufin kada a nada wani daban a mukaminsa.
“Ya ce idan mun gama aikin, zai ba kowannenmu Naira dubu 50. Amma bai ba mu ko kwabo ba a matsayin somin-tabi. Bayan mun kammala aikin, shi ne dan uwana ya yi fushi, ya ce mani bai kamata in tsoma kaina cikin irin wannan aika-aika ba. Shi ne fa ya sanar da babban wanmu abin da na aikata.” Inji shi.