Ya kashe maigida da matarsa saboda gidan haya

Ana zargin wani matashi mai suna Ime da ake wa lakabi da Shawa kan kashe  maigidan da yake haya mai suna Edem Akpan da matarsa mai suna Affiong saboda ba shi takardar ya bar masa gidan da ke unguwar Asukuo Eyo a birnin Uyo, hedkwatar Jihar Akwa Ibom.Bayanan da ’yar mamacin mai suna Emem Akpan […]

Ya kashe maigida da matarsa saboda gidan haya

Wani yanki daga cikin gidan da aka konaAna zargin wani matashi mai suna Ime da ake wa lakabi da Shawa kan kashe  maigidan da yake haya mai suna Edem Akpan da matarsa mai suna Affiong saboda ba shi takardar ya bar masa gidan da ke unguwar Asukuo Eyo a birnin Uyo, hedkwatar Jihar Akwa Ibom.
Bayanan da ’yar mamacin mai suna Emem Akpan ta yi wa Aminiya, sun nuna matashin, wanda ya kashe maigidan da matarsa kuma ya kona gidan, ba ya son biyan kudin hayarsa ne, idan lokaci ya yi. “Kodayaushe sai an kai ruwa rana kafin ya biya kudin hayarsa idan wa’adi ya kare. Wannan ne ya sanya babanmu ya gaji, ya ba shi takardar ya bar masa gida, shi kuma ya ji haushi ya rika neman fada”. Inji ta.
Ana nan, ranar nan, sai ya dauki adda ya far wa maigida da matarsa da sara, har sai da ya ga bayansu, daya bayan daya, daga nan sai ya banka wa gidan wuta.
Emem ta ci gaba da cewa, “Mun rika ganinsa yana kawo tsofaffin tayoyin mota gidan, amma duk ba mu farga da aniyarsa ba, har sai da ya sanya wa gidanmu wuta, kuma kafin ya sanya wutar, sai da ya sayo fetur mai yawa ya yayyafa wa gidan”.
Wata majiya kusa da makwabcin mamatan ta shaida wa Aminiya cewa da ma an tsinkaye shi yana cewa matukar aka matsa sai ya bar gidan, shi kuwa ya yi alwashin su ma sai sun bar duniya.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom Etim Dickson ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ana cigiyar wanda ake zargi da aikata laifin, kuma da zarar an kama shi za a gurfanar da shi gaban kuliya.