Ya kashe maigida da matarsa saboda kin cika alkawari

Wani matashi dan asalin Jihar Ebonyi ya shiga hannu bayan ya hallaka maigidansa  da matarsa wanda kuma Yayansa. Lamarin ya faru ne a Sango Ota a Jihar Ogun inda wanda ake zargin mai suna Okwudili Okoro ya hada baki da abokisa Kenneth wajen hallaka maigidan da matarsa. Wanda ake zargin ya ce sun yi yarjejeniya […]

Ya kashe maigida da matarsa saboda kin cika alkawari

Wani matashi dan asalin Jihar Ebonyi ya shiga hannu bayan ya hallaka maigidansa  da matarsa wanda kuma Yayansa. Lamarin ya faru ne a Sango Ota a Jihar Ogun inda wanda ake zargin mai suna Okwudili Okoro ya hada baki da abokisa Kenneth wajen hallaka maigidan da matarsa.

Wanda ake zargin ya ce sun yi yarjejeniya da  maigidansa Azuibuke Okoro wanda Yayansa ne inda ya yi masa dawainiyar kula da shagonsa na tsawan shekara 3.   Bayan ya shekara 3 yana yi masa hidimar kula da kasuwanci da lokacin sallamarsa ya yi sai maigidansa ya yi ta yi masa alkawari amma yana sabawa da hakan ya nemi taimakon abokinsa Kenneth  suka sayi adduna biyu daga nan suka nufi gidan maigidan da ke Sango Ota a Abeokuta suka tarar da shi yana karin kumallo tare da matarsa kafin ya ce uffan suka sassara shi suka hallaka shi tare da matar.

A cewar mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi wani makwabcin mamacin ne ya ankarar da rundunar inda suka dirar wa wadanda ake zargin suka damke shi  sai dai abokin ta’asarsa Kenneth ya tsere kuma rundunar na nemansa ruwa a jallo. 

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan jihar ya ba da umarnin tura wanda ake zargin sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar domin zurfafa bincike. Sannan tuni aka kai gawarwakin mamatan dakin ajiye gawarwaki na babban  asibitin Otta.