Ya kashe maigidansa a kan yunkurin yi masa fyade

Wani matashi dan kimanin shekaru 22, mai suna Eji Emmanuel ya kashe maigidansa mai suna Sylbanus Okoye mai kimanin shekara 39, saboda zargin maigidan nasa ya yi kokarin yin luwadi da shi.Eji Emmanuel ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne a karshen makon da ya gabata a lokacin da maigidansa ya yi kokarin […]

Ya kashe maigidansa a kan yunkurin yi masa fyade

?????????????????????????????????????????????????????????

Eji Emmanuel da ake zargi da kashe maigidansa OkoyeWani matashi dan kimanin shekaru 22, mai suna Eji Emmanuel ya kashe maigidansa mai suna Sylbanus Okoye mai kimanin shekara 39, saboda zargin maigidan nasa ya yi kokarin yin luwadi da shi.
Eji Emmanuel ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne a karshen makon da ya gabata a lokacin da maigidansa ya yi kokarin yi masa fyade yayin da yake kwance a gidansa da ke kan titin Ezemegbu da ke unguwar Okota a Legas.
Ya ce, “Ni dan rawa ne, wani abokina ne  mai suna Chukwudi ya yaudare ni zuwa Legas inda daga bisani ya sanya ni a harkar luwadi. A lokacin da na je kai wa maigidan abokin nawa kara, sai shi ma ya yaudare ni ya yi min fyade har sau biyu, inda daga bisani na kai kara ofishin ’yan sanda na Festac amma daga bisani sai ’yan sanda suka juya abin ya koma ni ake zargi da yin sharri. Nan take aka kulle ni tsawon mako biyu. Bayan na fito sai na tuntubi Okoye, a matsayinsa na shugaban ’yan kabilar Igbo na yankin Fastac, don ya taiamaka mini da kudin motar da zan koma gida Anambra, Sai ya ba ni Naira dubu biyar ya nemi na kwana a gidansa. Ina cikin  barci da dare, sai sadado ya shigo dakin da nake ya nemi yin luwadi da ni. Ni kuwa sai na ki. Da na ga ya dage sai ya yi mini da karfi, sai na dauki wata wuka da ya ba ni na yanki biredi na caka maka a wuya. Nan take sai ya fadi ni kuwa na gudu’.
Makwabtansu sun bayyana cewa Okoye, maigidan Emmanuel ne, sun dade tare a gida daya kuma maigidan ne ya bude masa wurin sayar da giya a unguwar.
Tuni ’yan sanda suka kame Eji Emmanuel, wanda suke zargi da daba wa maigidansa wuka a wuya inda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Ngozi Braide ta bayyana cewa ’yan sanda sun kama  Emmanuel a Anambara ta hanyar wayar  budurwarsa wacce yake kira da wayar Okoye a lokacin suna tare a Legas, kuma suna bincike don gano yadda abin yake inda da zarar sun kammala binciken za su kai lamarin kotu.