Ya kashe makwabcinsa da ya ba shi rancen Naira dubu 80  ya biya haya

Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja tana gudanar da bincike a kan wadansu mutum 3 da ofishinta na Suleja ya kama kan zargin kashe wani magidanci da binne gawarsa a wani kango. Marigayin mai suna Malam Abdullahi Liman da ke aiki a Hukumar Binciken Ma’adinai ta Kasa (RMRDC), Aminiya ta samu labarin cewa ya ranta wa […]

Ya kashe makwabcinsa da ya ba shi rancen Naira dubu 80  ya biya haya

Sufeto Janar Adamu Abubakar Muhammad

Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja tana gudanar da bincike a kan wadansu mutum 3 da ofishinta na Suleja ya kama kan zargin kashe wani magidanci da binne gawarsa a wani kango.

Marigayin mai suna Malam Abdullahi Liman da ke aiki a Hukumar Binciken Ma’adinai ta Kasa (RMRDC), Aminiya ta samu labarin cewa ya ranta wa daya daga cikin wadanda ake zargi da hallaka shi ne mai suna Adelawo Adedayo da ke kera tagar goran-ruwa, kuma suke haya a gida daya a Unguwar APC a Suleja, rancen Naira dubu 80 don ya biya hayar daki.

Majiyar ta ce marigayin ya bai wa wanda ake zargin rancen ne don ya cika kudin hayar bangaren da yake a gidan, bayan da mai gudan ya yi barazanar fitar da shi wata uku da suka gabata.

Haka bayanai sun ce wanda ake zargin ya mayar da bashin Naira dubu 20 daga cikin kudin da ya ranta, tare da alkawarin biyan ragowar Naira dubu 60 a ranar Talata da ta gabata, ranar da lamarin kisan ya faru da dare.

Majiyarmu ta ce “An gano an aikata kisan ne bayan matar marigayin, wadda ke zaune a Minna tare da ’ya’yansu 4 ta yi wa mijinta waya washegari Laraba da safe; saboda bai yi mata waya ba yadda ya saba yi  duk safiya ba. Daga nan ne ta ankarar da wani dan uwanta da ke Suleja, wanda ya je gidan don tantace halin da mijinta ke ciki.”

Bayanai sun ce akwai wani abokin marigayin da suka dawo daga wurin aiki tare, wanda ya tuko shi a motarsa har zuwa unguwar a yammacin ranar da lamarin ya faru. Sai dai da ya nemi wayarsa washegari da safe don su wuce ofis sai wanda ake zargin ya amsa wayar, inda ya shaida masa cewa marigayin ya kaura daga gidan kuma ya bar wayarsa bai tafi da ita ba.

“Abokin nasa ya garzaya gidan, inda ya tarar dakin marigayin a rufe sannan ga jini a kofar dakin. Daga nan ne ya kai lamarin ga ’yan sanda, wadanda suka gayyaci daukacin mazauna gidan zuwa ofishinsu; kowa ya rubuta jawabi kafin suka sake dawowa gidan don yin bincike a dakin kowa. Ana binciken ne wanda ake zargin ya fice daga gidan a guje, kuma bayan an kamo shi ne aka bude dakinsa, inda aka gano shimfidar marigayin a cikin dakin an nade jike da jini,” inji majiyarmu.

Babban Jami’in ’Yan sandan Suleja, CSP Yakubu Isa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan an kawo wanda ake zargin ofishinsu, ya tabbatar musu cewa shi ya aikata kisan tare da taimakon budurwarsa da ta kawo masa ziyara a daren da kuma kanenta, inda suka dauki gawar zuwa wani killataccen fuloti da ba a gina ba suka binne, daga nan aka wuce da shi wajen aka tono shi.

Ya ce sun mika mutum ukun ga Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na ofishinsu da ke Minna don ci gaba da yin bincike a kan lamarin.

 

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta