Ya kashe matar maƙwabcinsa kan sharar tsakar gida

Bayan ya kashe su sai ya ɓoye gawarsu a cikin wata ƙatuwar jaka

Ya kashe matar maƙwabcinsa kan sharar tsakar gida

Wani mutum ya shiga hannun hukuma kan kisan matar maƙwabcinsa da ɗanta saboda shara a yankin Lekki da ke Jihar Legas.

Lamarin ya auku ne bayan sa-in-sa da aka samu a tsakaninsu a kan sharar harabar gidan da dukkansu suke zaune.

Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce rikicin ya munana, har ta kai ga mutumin ya yi amfani da makami ya hallaka matar maƙwabcin nasa da ɗanta.

Bayan ya kashe su sai ya ɓoye gawarsu a cikin wata ƙatuwar jakar “Ghana Must Go”.

Hundeyin ya ce bayan samun rahoto ne ’yan sanda suka kai same da dare suka kamo shi.

Ya ce, “an gano gawar Gloria da ɗan nata, an kai Babban Asibitin Epe inda aka ajiye a mutuware domin gudanar da bincike.”

A wani wani labari kuma, an tsinci gawar wani ɗan shekara 54 a yankin Agege da ke jihar.

An tsinci gawar tasa ce a rataye a jikin silin a cikin wani suto, lamarin da ya sa ake zargin shi ne ya rataye kansa.