Ya kashe matar wansa bayan ya yi mata fyade

Wani matashi da ake zargi da kashe matar dan uwansa bayan ya yi mata fyade ya shiga komar ‘yan sanda a jihar Zamfara. “Ko da jami’an ‘yan sandan suka isa wajen sun tarar da marigayiyar mai suna Hauwa cikin jini bayan wanda ake zargin ya sanya adda ya sassare ta. “Daga nan ne aka kai […]

Ya kashe matar wansa bayan ya yi mata fyade

Fyade

Wani matashi da ake zargi da kashe matar dan uwansa bayan ya yi mata fyade ya shiga komar ‘yan sanda a jihar Zamfara.

“Ko da jami’an ‘yan sandan suka isa wajen sun tarar da marigayiyar mai suna Hauwa cikin jini bayan wanda ake zargin ya sanya adda ya sassare ta.

“Daga nan ne aka kai ta Asibitin Kwararru na Yariman Bakura inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta”, a cewar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kakakin Rundunar SP Muhammad Shehu ya ce matashin ya amsa cewa ya yi wa matar wansa fyade sannan ya kashe ta.

A cewarsa a ranar 15 ga watan Yuni, wasu mazauna unguwar Damba a garin Gusau suka sanar da ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ya kashe matar dan uwansa wanda yake yaya a gare shi.

Ya kara da cewa mijin matar ba ya gari. “Ya shaida mani ta waya cewa wanda ake zargin ya dade yana yin barazanar kashe marigayiyar.

“Yanzu haka muna jiran mijin matar ya zo ya rubuta jawabinsa kafin mu kai ga gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu”, inji shi.

Ya ce wanda ake zargin, mai shekaru 25 dan asalin karamar hukumar Maradun ne a jihar Zamfara.

Marigayiyar Hauwa Shehu ta rasu ta bar ‘yaya biyu ciki har da na goye mai watanni tara.